Hajjin Bana: Za a Rufe Saudi Nan da Kwana 4, Maniyyata 15000 Ba Su Bar Najeriya Ba

Hajjin Bana: Za a Rufe Saudi Nan da Kwana 4, Maniyyata 15000 Ba Su Bar Najeriya Ba

  • Zuwa yanzu mutane 62,000 aka dauka daga Najeriya zuwa Saudi Arabiya domin su yi aikin hajji
  • Akwai ragowar maniyyata sama da 10, 000 da jiragensu ba su tashi, su na jiran hukumar alhazai
  • NAHCON ta tabbatar da babu wanda za a bari ba tare da ya sauke farali kamar yadda ya yi niyya ba

Abuja - A lokacin da ake bada sanarwar ganin wata, akwai maniyyatan Najeriya da adadinsu ya zarce 15, 000 da har yanzu ba su tafi Saudiyya ba.

Rahoto ya zo daga Daily Trust cewa hukumar kula da aikin hajji ta kasa (NAHCON) ta na da mutane jibge a yanzu da ba a kai su kasa mai tsarki ba.

Akwai maniyyata da-dama da su ke kwana a sansanin mahajjata a dalilin rashin cika alkawarin hukuma da kamfanonin jiragen da ke jigilarsu.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An yi ram da wasu mazauna Qatar, rikakkun 'yan safarar kwaya a wata jiha

Hajjin Bana
Wasu wajen aikin hajji a Saudi Arabiya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Hakan ya jawo wasu maniyatta su ka koma kwana a masallatai da cikin farfajiyar filin tashin jirgi. NAHCON ta yi alkawari kowa zai yi aikin hajji.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Arik Air bai dauki mutanensa ba

Rahoton ya ce kamfanin Arik Air ya iya daukar mutane 300 ne daga cikin fasinjoi 7000 da aka ba shi.

Hukumar NAHCON ta yi alkawari jirgin saman zai cigaba da jigilar fasinjoji a jiya. Sai dai bincike ya nuna har yanzu fasinjojinsa ba su bar Najeriya ba.

Akwai maniyyatan da sun shafe kwanaki biyar su na jiran a dauke su zuwa Saudiyya amma har yau babu labari, hakan zai iya jawo matsala.

Idan ba a dauki matakan gaggawa ba, maniyatta fiye da 6, 000 ba za su sauke farali a bana ba.

Halin da ake ciki a yau

Dole sai Arik Air ya dauki fasijoji 1, 500 a kowace rana daga yau zuwa lokacin da za a rufe filin jirgin Saudiyya idan ana so a dauke duka ‘Yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Maganin barna: Uwa ta cije, ta hana danta jakar makaranta, ta mika masa buhun siminti

Shugaban kungiyar AHUON, Alhaji Nasidi Yahaya ya ce an dauki hayar wani jirgin Max Air domin a iya daukar maniyattan da har yanzu ba su tashi ba.

Legit.ng Hausa ta fahimci an kira wasu cikin maniyyata daga kananan hukumomin Kaduna tun Juma’a, amma sai daren yau su ka shiga kasar Saudi.

Wata majiya ta shaida mana mutanen Sabon Gari su na sansanin mahajjatan Kaduna tun Juma’a, amma wasu cikinsu ba su isa Saudi ba sai daren Litinin.

Pantami ya samu lambar girma

Rahoto ya zo a karshen makon jiya cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya sake samun lambar yabo ta gwanintar aiki daga gidan talabijin Qausain.

Tashar Qausain ta ce ta ba tsohon ministan wannan lambar yabo ne saboda sauyin da ya kawo a bangarori da dama a lokacin ya na gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng