Dakarun Sojin Sama Sun Yi Luguden Wuta Kan Kwamandojin ISWAP a Borno
- Dakarun sojin saman Najeriya sun yi luguden wuta kan mayaƙan ƙungiyar ta'addanci ta ISWAP a jihar Borno
- A yayin harin dakarun sojojin sun tura wasu manyan kwamandojin ƙingiyar ta'addancin har guda biyu zuwa inda ba a dawowa
- Wasu daga cikin mayakan ƙungiyar sun baƙunci lahira a harin yayin da wasu da dama suka arce bayan sun samu munanan raunika
Jihar Borno - Dakarun sojojin saman Najeriya sun halaka wasu kwamandojin ƙungiyar ta'addanci ta Islamic State in West Africa Province (ISWAP).
Jaridar The Cable ta kawo rahoto cewa dakarun sojin saman sun halaka kwamandojin ne guda biyu a kusa da yankin tafkin Chadi.
Zagazola Makama, wani masani kan harkokin tsaro da ya mayar da hankali kan yankin tafkin Chadi, ya bayyana cewa kwamandojin ƙungiyar sun sheƙa barzahu ne a wani harin sama da dakarun sojin suka kai musu.
Ya ƙara da cewa a yayin harin wanda dakarun sojin saman suka kai daban-daban a ƙararmar hukumar Marte ta jihar Borno a ranar Asabar, Malam Bello da Musa Modu sun baƙunci lahira tare da wasu mayaƙansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojin saman sun farmaki maɓoyar ƴan ta'addan
Makama ya ambato majiyoyi na bayyana cewa an kai hare-haren na sama ne bayan bayanan sirri sun tabbatar da ƴan ta'addan suna ɓoye a wajen.
Binciken da aka gudanar domin duba nasarar da aka samu wajen kai harin, ya tabbatar da cewa kwamandojin na ISWAP da mayaƙansu sun yi bankwana da duniya.
Wasu daga cikin mayaƙan da suka samu raunika daga harin sun arce zuwa yankin Tudun Wulgo da Ngilewa.
Kwamandan rundunar haɗin guiwa ta Joint Task Force, Manjo Janar Ibrahim Ali, ya ɗora masa alhakin kakkaɓe mayaƙan Boko Haram da na ISWAP daga yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Da Dumi-Dumi: Mummunan Hatsarin Mota Ya Ritsa Da Fasinjoji Da Dama a Wata Jiha, Rayuka Masu Yawa Sun Salwanta
'Yan Boko Haram Sun Yi Wa Mutane Yankan Rago a Borno
A wani labarin na daban kuma, ƴan ta'addan ƙungiyar Boko Haram sun halaka wasu bayin Allah aƙalla mutum 15 a wasu hare-hare da suka kai a ƙauyukan jihar Borno.
Ƴan ta'addan dai sun halaka mutanen ne ta hanyar yi musu yankan rago a hare-haren da suka kai.
Asali: Legit.ng