An Ga Watan Dhul Hijjah a Saudiyya: Muhimman Ranakun da Ya Kamata Duk Musulmi Ya Kiyaye
- Kasar Saudiyya ta sanar da ganin jinjirin watan Dhull Hijjah na wannan shekarar, za a fara aikin Hajjin bana
- Tuni Musulmai daga sassan duniya suka fara tafiyar ziyara zuwa kasar domin gudanar da aikin na Hajji
- Ya zuwa yanzu, jirage daga Najeriya sun sauka Saudiyya, duk da an samu tsaiko a tashin jiragen wasu jihohi
Kasar Saudiyya - Kotun kolin kasar Saudiyya ya sanar da ganin jinjirin watan Dhul Hijjah da ake gudanar da ayyuka Hajji, Arab News ta ruwaito.
Bana ma bata sauya zane ba, za a fara gudanar da shirye-shiryen ayyukan Hajjin bana daga ranar 1 ga watan Dhul Hijjah, wanda ya yi daidai da ranar 19 ga watan Yuni.
Hakan na nufin cewa, a ranar 26 ga watan Yuni da ya yi daidai da 8 ga watan Dhul Hijjah ne za a fara gudanar da aikin Hajji, wanda dukkan Musulmin da suka samu dama za su fara.
Hakazalika, a ranar 27 ga watan Yuni, wanda ya yi daidai da 9 ga watan Dhul Hijjah za a yi tsayuwar Arafah, kamar yadda addinin Islama ya tanada.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Musulmin da ba su samu damar zuwa aikin Hajjin bana ba, za su yi bikin Sallar Idi ne a ranar Laraba 28 ga watan Yuni da ya yi daidai da 10 ga watan na Dhull Hijjah.
Aikin Hajji ga Musulmi a duniya
Kamar yadda addinin Islama ya tanada, ya wajaba a kan dukkan Musulmin da ya samu damar zuwa ziyarar Hajji ya gudanar da ibadar sau daya a rayuwarsa.
Aikin hajji, na daya daga cikin rukunan addinin Islama guda biyar wadanda suka hada da; Shahada, Sallah, Azumi, Zakkah sai na biyar din kuwa Hajji.
A halin da ake ciki, Musulmai daga kasashen duniya sun fara dura a kasar Saudiyya domin gudanar da wannan ibada mai muhimmanci.
Yadda Alhazan Najeriya Mata 75 Suka kare a Asibitocin Makkah da Madina
Hukumar kula da alhazai ta kasa (NAHCON) ta bayyana cewa kawo yanzu an kwantar da maniyyata mata 75 masu ɗauke da juna biyu a asibitocin Makkah da Madina.
Jaridar Punch ta rahoto ce an garzaya da maniyyatan masu ciki Asibiti ne domin kula da lafiyarsu sakamakon abinda su ke dauke da shi kuma ga aikin Hajji.
NAHCON ta ce mafi yawan maniyyata sun sa kafa sun shure shawarwari da kuma wayar da kan da aka musu kan cewa duk mace mai juna biyu ta haƙura da tafiya aikin Hajjin bana.
Asali: Legit.ng