Ba Na Cikin Jerin Sunayen Mutanen da EFCC Ke Nema Ruwa a Jallo, Inji Gwamna Matawalle
- Bello Matawalle, tsohon gwamnan jihar Zamfara, ya musanta cewa hukumar EFCC na nemansa, inda ya karyata labarin da jaridar Nigerian Tribune ta wallafa
- Mai taimakawa Matawalle kan harkokin yada labarai ya bayyana rahoton a matsayin na karya, wanda aka buga da nufin bata sunan tsohon gwamnan
- Ya kuma bayyana cewa, EFCC na bin ka’idojin aiki kafin alanta neman wani, inda ya nemi jaridar ta nemi afuwar gwamnan
Jihar Zamfara – Bello Matawalle, tsohon gwamnan jihar Zamfara, ya karyata rahotannin da ke cewa hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta ce na nemansa.
Jaridar Nigerian Tribune ta buga wani labari a ranar Lahadi, 18 ga watan Yuni, 2023, tana mai cewa EFCC ta alanta neman Matawalle ruwa a jallo.
Sai dai a wata sanarwa da mai taimaka wa tsohon gwamnan kan harkokin yada labarai Lawal Umar ya fitar, ya bayyana labarin a matsayin na karya kuma wanda aka buga da nufin bata sunan Matawalle, kamar yadda TVC ta ruwaito.
Umar ya kara da cewa rahoton da jaridar Nigerian Tribune ta fitar ba shi da tushe balle makama kuma ba tabbas bai da nagarta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
EFCC ba ta amfani da ra’ayoyin jama’a, in ji Matawalle
Umar ya kara da cewa hukumar EFCC a matsayinta na babbar hukumar tabbatar da doka da oda, tana bin ka’ida wajen gudanar da ayyukanta.
A cewarsa, EFCC ba ta aiwatar da aikinta bisa tunzurawar mutane ba bisa ka’ida ba kana ba tare da kwakkwaran hujja da bin ka’idojin shari’a ba.
Ya kuma kara da cewa Matawalle yana nan tun dawowarsa daga duba likita a ranar 26 ga watan Mayun 2023, kuma babu wata hukuma da ta tabbatar da cewa tana neman sa.
“Tsohon Gwamna Bello Matawalle yana nan tun bayan dawowarsa a ranar 26 ga watan Mayun 2023 daga ganin likita kuma babu wata hukuma da ta tabbatar da cewa tana nemansa.”
Ku nemi afuwar tsohon gwamna
Daga karshe, Umar ya yi kira ga jaridar da ta janye labarin tare da ba Matawalle hakuri da neman afuwarsa.
Ita kanta hukumar EFCC ta ce tabbas bata neman tsohon gwamnan kamar yadda muka ruwaito muku baya.
Asali: Legit.ng