Mutane Sun Dimauta Yayin Da Aka Tsinci Jariri Kwance Cikin Tsumma a Jihar Kaduna

Mutane Sun Dimauta Yayin Da Aka Tsinci Jariri Kwance Cikin Tsumma a Jihar Kaduna

  • Mutane sun shiga damuwa bayan samun wani jariri kwance a cikin tsumma ba tare da kaya a jikinsa ba a unguwar Mu'azu da ke Kaduna babban birnin jihar
  • Jaririn kamar yadda aka tabbatar an tsince shi ne a wani kango da ba a kammala ba a ranar Asabar 17 ga watan Yuni da misalin karfe takwas na safe
  • Wani daga cikin 'yan sa-kai da bai so a ambaci sunansa ba ya bayyana cewa jararin bisa dukkan alamu yana cikin koshin lafiya kuma ya ba da rahoton ga 'yan sanda

Jihar Kaduna - Mutane sun dimauta bayan da aka tsinci jinjiri a wani kangon da ba a karasa ba a unguwar Mu'azu da ke cikin birnin Kaduna.

Wani mutumin kirki ne ya tsinci jinjiri a ranar Asabar 17 ga watan Yuni tare da mika shi ga daya daga cikin 'yan sakai a jihar da misalin karfe 8 na safe.

Kara karanta wannan

Yadda Aka Ba Hammata Iska Tsakanin Jami’in NSCDC Da Dan Bautar Kasa a Kan Abinci

An tsinci jariri a cikin kango a jihar Kaduna
Wani Jariri Da Aka Tsinta. Hoto: Linda Ikeji.
Asali: Facebook

Daily Trust ta tattaro cewa jinjirin da aka tsinta yana cikin tsumma babu komai a jikinsa sai kunzugu, yayin da jinjirin ke cikin wani mummunar hali.

Daya daga cikin 'yan sakai din da suka karbi jinjirin wanda ya bukaci a boye sunansa ya ce an samu jinjirin ne a kusa da wani kango kuma a cikin tsumma.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar matashin:

"Yasasshen jinjirin an tsince shi ne a Unguwar Mu'azu kusa da wani kango da ba a kammala ba.
"Akwai alamun jinjirin na cikin koshin lafiya, kuma muna iya bakin kokarinmu don ganin mun kawo agaji.
"Sannan na kai rahoton wannan al'amari ofishin 'yan sanda ta Kabala ta Yamma."

Kokarin jin ta bakin rundunar 'yan sandan jihar yaci tura saboda rashin samu lambar wayarsu.

Mazauna Wata Unguwa A Jihar Kaduna Sun Koka Kan Rashin Wuta Na Tsawon Shekaru 8

Kara karanta wannan

Innalillahi: Makiyaya da manoma sun kaure a jihar Arewa, an hallaka mutum 13 nan take

A wani labarin, mazauna Unguwar dan Lawal da ke Kurmin Kogi da ke jihar Kaduna sun koka kan yadda suka shafe shekaru 8 babu wutar lantarki.

Suka ce matsalar ta fara ne tun shekarar 2015 bayan tafka ruwa mai yawa a yankin da ya yi sanadiyar lalacewar sandunan wutar lantarki.

Mazauna unguwar wacce ke cikin karamar hukumar Ikara ta jihar sun kuma koka cewa bayan lalacewar barayi sun sace wayoyin cikin na'urar ba da wurtar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.