Fada Ya Kaure Tsakanin Jami’in NSCDC Da Dan Bautar Kasa a Kan Abinci

Fada Ya Kaure Tsakanin Jami’in NSCDC Da Dan Bautar Kasa a Kan Abinci

  • Sabani ya gibta tsakanin wani jami'in hukumar NSCDC da dan bautar kasa a wajen wani taro a Abuja
  • Mai yi wa kasa hidima da jami'in tsaron sun yi cacar baki a kan rabon abinci lamarin da ya kaisu ga ba hammata iska
  • Wani jami'in NSCDC ya nuna fushinsa kan yadda sauran takwarorinsu da ke wajen suka tsaya suna kallo ba tare da sun ladabtar da dan NYSC din ba

Abuja - Rahotanni sun kawo cewa sabani ya shiga tsakanin wani jami'in hukumar NSCDC da wani dan bautar kasa (NYSC) a ranar Asabar, 17 ga watan Yuni kan abinci a wajen wani taro a Abuja.

Sashin kula da wuraren shakatawa na hukumar babban birnin tarayya ne ya shirya taron domin bikin ranar yaki da hamada da fari ta duniya na 2023 tare da kaddamar da kamfen din dashen itatuwa na shekara-shekara.

Kara karanta wannan

An Zabo Mana Bala'i: Kanawa Sun Fusata Da Rushe-Rushen Abba, Sun Hana Rushe Gidajensu

Jami'an NSCDC
Fada Ya Kaure Tsakanin Jami’in NSCDC Da Dan Bautar Kasa a Kan Abinci Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa ba don wasu mahalarta taron sun gaggauta shiga lamarin ba, da fadan ya yi muni domin sauran yan bautar kasa sun so shigarwa takwaransu wajen fada da jami'in na NSCDC.

Taron wanda aka gudanar a ofishin sashin da ke cikin yankin sojoji a Asokoro, ya cika da baki, wanda yawancinsu suka tafi gida a fusashe saboda sashin ya boye abinci da lemu da aka tanada saboda baki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda fadan ya fara

Fadan ya fara ne lokacin da wani jami'in NSCDC, sanye da kayan aiki ya yi kokarin karbar wata jaka da ke dauke da kwanukan shinkafa da lamuka daga hannun wani dan bautar kasa.

Dan bautar kasan wanda ya nemi a sakaya shi, ya ce ya yi kokarin yi wa jami'in bayani cewa abincin na takwarorinsa da aka gayyana zuwa taron ne amma ya ki ji.

Kara karanta wannan

“Neman Halal”: Matashiya Mai Ji Da Tsantsar Kyau Ta Kama Sana’r Tuwo, Bidiyonta Ya Yadu

"Daya daga cikin ma'aikatan ya kira ni don na je na karbi abinci, don haka na ga jakan na dauka amma wasu jami'an hukumar NSCDC uku suka zo suka kwace jakar daga hannuna. Na tambayi dalilinsu na kwace jakar daga hannuna saboda an sanar da ni cewa na yan bautar kasa ne.
"Kafin na san me ke faruwa, wani jami'in NSCDC ya fara yi mun gargadin cewa na shiga hankalina sannan na ce shin saboda abinci ne kake nuna mani yatsa da cewa na shiga hankalina?
"Na fada mashi cewa shima ya shiga hankalinsa, sai ya ce zai yi mani duka, amma na fada masa cewa ba zai iya dukana ba. Kafin na san me ke faruwa ya fara buguna, don haka muka fara fada."

Ya za a yi dan NYSC ya yi jayayyan abinci da wanda ke sanye da inifam, jami'in NSCDC ya nuna fushinsa

Nigerian Tribune ta nakalto daya daga cikin jami'an NSCDC din yana cewa:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Ta Bada Umarni a Ruguza Gidaje, Rigima Ta Kaure da ‘Yan Unguwa

"Ba daidai bane wannan matashin da ya kira kansa da dan bautar kasa ya dunga jayayyan abinci da daya daga cikin mutanenmu.
"Damuwana ma ba abincin bane illa yadda yake fada da wani mutum da ke sanye da inifam. Na yi fushi da wasu daga cikin jami'anmu da suka tsaya suna kallon abun da ke faruwa maimakon lallasa gayen."

Ina tursasawa matata yi wa yan uwa na sanatoci alfarma - Sanata Bulkachuwa

A wani labarin mun ji cewa, Adamu Bulkachuwa, sanata mai wakiltan Bauchi ta arewa, ya yi wani gagarumin fallasa game da harkokin matarsa a matsayinta na mai shari'a.

Dan majalisar na Bauchi ya bayyana cewa Zainab Bulkachuwa, matarsa, ta yi amfani da mukaminta a matsayin mai shari'a wajen yi wa takwarorinsa a majalisar dattawa alfarma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng