Cire Tallafin Man Fetur: Gwamnan Neja Zai Samar Da Motocin Kyauta a Makarantun Gwamnati
- GwamnaMohammed Umar Bago na jihar Neja na shirin samar da mafita ga daliban jihar yayin da yan Najeriya ke kokawa kan cire tallafin man fetur
- Domin ragewa daliban jihar radadin tsadar kudin mota, gwamnatin Neja za ta samar da motocin kyauta da zai dunga jigilar dalibai
- Daliban makarantun gwamnati a fadin jihar sune za su ci gajiyar wannan shiri kamar yadda gwamnan ya bayyana a ranar Juma'a
Niger - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bayyana shirin gwamnatinsa na samar da motocin kyauta ga dalibai a makarantun gwamnatin jihar domin karfafa masu gwiwa da duba yaran da suka daina zuwa makaranta.
Bago ya ce suna shirin daukar wannan mataki ne saboda tsadar abun hawa sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi, Daily Trust ta rahoto.
Ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a yayin da ya karbi bakuncin jami'an hukumar NECO karkashin jagorancin shugabansu, Farfesa Ibrahim Wushishi a gidan gwamnati da ke garin Minna, rahoton Punch.
Gwamnan ya yi bayanin cewa samawa yara da ke matakin firamare ababen hawa na kyauta zai "karfafawa yara gwiwar zuwa makaranta a matakin firamare sannan ya rage radadin cire tallafin man fetur."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Bago ya baiwa hukumar NECO gagarumin aiki
Bago ya kuma yi kira ga hukumar jarrabawar da ta tallafawa jihar wajen magance matsalolin yaran da ba sa zuwa makaranta, musamman yara mata.
Gwamnan ya kuma bayar da shawarar cewa ya kamata NECO ta samar da hanyoyin koyar da sana'o'i a tsarin karatu domin dalibai su zamo masu dogaro da kai.
Ya bayar da umurni cewa a dunga biyan naira miliyan 30 duk wata domin warware bashin da NECO ke bin jihar.
"A duba lamarinmu": Yan Abuja sun roki shugaban kasa Tinubu da ya basu minsitan Abuja
A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa yan asalin Abuja sun mika kokon bararsu a gaban shugaban kasa Bola Tinubu inda suka roki ya basu kujerar ministan babban birnin tarayya.
Yan asalin yankin wadanda suka ce an dade ana cutarsu sun ce babu yadda za a yi a ci gaba da dauko masu bakin haure domin jibantar lamuransu.
Asali: Legit.ng