Dan Majalisar dokokin Jihar Kaduna Ya Rasu Kwana Hudu Bayan Rantsuwa
- An shiga jimami a jihar Kaduna bayan wani ɗan majalisar dokokin jihar ya koma ga mahaliccinsa a ranar Asabar
- Madami Garba Madami ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Chikun ya yi bankwana da duniya ne bayan fama da rashin lafiya
- Ɗan majalisar ya rasu ne kwana huɗu bayan an rantsar da sabbin ƴan majalisar dokokin jihar, rantsuwar da bai samu halarta ba
Jihar Kaduna - Ɗan majalisar da ke wakiltar ƙaramar hukumar Chikun a majalisar dokokin jihar Kaduna, Madami Garba Madami, na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya riga mu gidan gaskiya.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa ɗan majalisar ya rasu ne a safiyar ranar Asabar, 17 ga watan Yuni a wani asibiti inda ake duba lafiyarsa.
Mamacin ya taɓa riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukumar Chikun da kwamishinan tsare-tsare da kasafin kuɗi. Ya kuma taɓa zama mai bayar da shawara kan harkokin siyasa ga tsohon gwamnan jihar Patrick Yakowa.
Ɗan majalisar ya rasu kwana huɗu bayan an rantsar da sabbin ƴan majalisar dokokin jihar
Idan ba a manta ba dai an rantsar da ƴan majalisar dokokin jihar Kaduna ta 10, a ranar 13 ga watan Yunin 2023, rantsuwar da marigayin bai samu halarta ba saboda rashin lafiyar da yake fama da ita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani majiya a yankin ya tabbatar da rasuwar ɗan majalisar inda ya bayyana mutuwarsa a matsayin abun baƙin ciki babba.
Haka kuma, wani mai riƙe da muƙamin sarauta a ƙaramar hukumar Chikun, Ibrahim Saleh Ardon Ardodin, ya tabbatar da rasuwar mamacin inda ya aike da saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin.
Gwamnan jihar Ƙaduna, Mallam Uba Sani, ya aike da saƙon ta'aziyyarsa ga ƴan uwa da iyalan mamacin da al'ummar ƙaramar hukumar Chikun, cewar rahoton Channels tv.
Dan Majalisar Dokokin Jihar Borno Ya Bar Duniya
Dan Sandan Da Ya Dawo Da $800 Na Wata Hajiya a Katsina, Ya Samu Kyautar Da Ba Zai Taba Mantawa Da Ita Ba a Rayuwarsa
A wani labarin na daban kuma, wani ɗan majalisar dokokin jihar Borno, ya koma ga mahaliccinsa bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Mr Nuhu Clark ya yi bankwana da duniya ne a ƙasar India inda ya je jinya bayan ya yi fama da jinyar rashin lafiya.
Asali: Legit.ng