Gwamna Lawal Na Zamfara Ya Gana da Shugaban Rundunar Tsaro a Abuja
- Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ziyarci hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Lucky Irabor a Abuja
- Gwamnan ya roki karin dakarun soji a jihar Zamfara da kuma goyon baya domin kawo karshen ayyukan 'yan bindiga
- Bayanai sun nuna tun bayan kama aikin sabon gwamnan, yan bindiga suka maida wasu garuruwa wurin zuwa farauta
FCT Abuja - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya buƙaci ƙarin goyon bayan rundunar sojin Najeriya domin kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi jiharsa.
Gwamna Lawal ya roƙi karin yawan sojoji da kuma goyon baya ranar Jumu'a yayin da ya kai ziyara ga babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor, a hedkwatar tsaro ta ƙasa da ke Abuja.
Channels tv ta rahoto cewa haka na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ranar Jumu'a, 16 ga watan Yuni, 2023.
Ya ce wannan ziyara da gwamna Lawal ya kai wa Irabor na ɗaya daga cikin matakan da yake ɗauka da nufin dawo da zaman lafiya da tsaro a jihar Zamfara.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jaridar Leadership ta rahoto kakakin gwamnan na cewa:
"Gwamna Lawal ya kai ziyara hedkwatar tsaro ta ƙasa domin yaba wa rundunar soji bisa yaƙin da suke da 'yan ta'adda a jihar Zamfara."
"Ya yi ganawar sirri da babban hafsan tsaro, Janar Lucky Irabor, domin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi tsaro da kuma lalubo mafita ta gaba."
"Hakan na cikin matakan gwamnatinmu ɗa nufin nuna wa gwamnatin tarayya nauyin da ya rataya a kanta dangane da tsaron cikin gida, wanda ya ƙunshi hukumar soji."
Gwamna Lawal ya shiga damuwa
Idris ya ƙara da cewa mai girma gwamna ya shiga damuwa matuƙa sakamakon ƙara tabarbarewar tsaro a wasu yankunan jihar Zamfara.
A cewarsa, gwamnan na aiki tuƙuru da haɗin kan masu ruwa da tsaki a hukumomin tsaron Najeriya domin tabbatar da tsaro ya inganta a jihar Zamfara.
Tun lokacin da Dauda Lawal ya kama aiki a matsayin gwamna, wasu yankunan juhar Zamfara suka zama wuraren farautar 'yan bindiga, hare-hare suka ƙara yawaita.
Kotu Ta Jingine Hukuncin da Ya Tsige Sufeta Janar Na Yan Sanda, Usman Baba
A wani rahoton kuma Babbar Kotun tarayya ta jingine hukuncin da ta yanke a watan Mayu, 2023 na tsige IGP Usman Baba daga kan mukaminsa
A ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni, 2023, Alkalin Kotun ya ce Kotu na da hurumin sauya hukuncin da ta yanke idan ta gano akwai lauje cikin naɗi a zaman shari'a.
Asali: Legit.ng