Shugaba Tinubu Ya Gana da Tsohon Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle a Villa
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da Aliko Ɗangote, shugaban kamfanin Ɗangote Group a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja
- Haka nan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ziyarci shugaba Tinubu a Villa ranar Jumu'a, 16 ga watan Yuni
- Matawalle ya ce yana da yakinin cewa Tinubu zai zama shugaban kasan da ba'a taɓa kamarsa ba a Najeriya
FCT Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi bakuncin shugaban kamfanin Ɗangote Group, Alhaji Aƙiko Ɗangote, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa Ɗangote ya kaucewa zantawa da yan jaridan gidan gwamnati bisa hujjar cewa zai sake dawowa Villa a mako mai zuwa.
A rahoton Punch, Ɗangote ya ce a mako mai zuwa zai sake ziyartar shugaba Tinubu tare da fitaccen Attajirin nan na duniya kuma shugaban kamfanin Bill and Melinda Gates Foundation, Bill Gates.
Matawalle ya gana da shugaba Tinubu
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya kai wa shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ziyara a Ofishinsa da ke Villa ranar Jumu'a, 15 ga watan Yuni.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da yake hira da manema labarai, Matawalle ya kwatanta wannan ziyara da ya kai wa Tinubu da, "Ziyarar ɗa ga mahaifinsa."
Ya ce shugaba Tinubu ya fara nuna wa duniya cewa yana da duk wata kwarewa da ake buƙata ta jan ragamar Najeriya.
Tinubu zai kafa tarihi - Matawalle
Matawalle ya kara da nuna yaƙinin cewa Tinubu zai kafa tarihin zama shugaban ƙasan da ba'a taɓa kamarsa ba a tarihi.
"Komai na tafiya daidai zuwa yanzu, kunga yadda shugaban kasa ya kinkimo aiki tun farko, to wannan ba sabon abu bane a wurinsa, shugaba ne nagari mai tsaruka masu kyau, zai cika alƙawurran da ya yi a kamfe."
"Bayan ganin kamun ludayinsa, da yawan mutane sun aminta cewa Najeriya zata zama ƙasar da ba bu kamarta a nahiyar nan. Ina da yaƙinin Asiwaju zai zama shugaban da ba'a taɓa kamarsa ba a kasar nan."
- Bello Matawalle.
Gwamna Radda Ya Jagoranci Gwamnonun Arewa Sun Gana da Tinubu a Villa
A wani labarin kuma Gwamnonin Arewa maso Yamna sun gana da shugaba Tinubu kan abinda ya shafi al'umma a jihohinsu.
Karkashin jagorancin gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, gwamnonin sun faɗa wa Tinubu matakan da suke ɗauka don zaman lafiya ya dawo a yankinsu.
Asali: Legit.ng