Dangote, Bill Gates Za Su Gana Da Tinubu A Ranar Litinin

Dangote, Bill Gates Za Su Gana Da Tinubu A Ranar Litinin

  • Ana saran a ranar Litinin 19 ga watan Yuni, shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote da shugaban kamfanin Microsoft, Bill Gates za su kai ziyara ga Shugaba Tinubu
  • Alhaji Aliko Dangote shi bayyana haka a ranar Juma'a 16 ga watan Yuni, inda ya ce ya zo ne kawai don sanar da shugaban kasar ziyarar ta su a ranar Litinin mai zuwa
  • Shugaba Bola Tinubu a kwanannan ya na ganawa da manya-manyan masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci da zuba jari don inganta tattalin arzikin Najeriya

FCT, Abuja - Shahararrun masu kudin duniya Alhaji Aliko Dangote da Bill Gates za su ziyarci shugaban kasa, Bola Tinubu a ranar Litinin 19 ga watan Yuni a fadarsa da ke Abuja.

Dangote ne ya bayyana haka bayan ganawar sirri da Shugaba Tinubu a fadarsa a yau Juma'a 16 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Ɗangote da Tsohon Gwamnan Zamfara a Villa, Ya Yi Jawabi Mai Jan Hankali

Dangote da Bill Gates za su kai ziyara ga Shugaba Tinubu
Aliko Dangote Da Bill Gates. Hoto: Toumai Web Medias.
Asali: UGC

Dangote ya bayyana ranar da za su kai ziyarar da Bill Gates fadar Shugaba Tinubu

A cewarsa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ba na zo ne don wani abu mai yawa ba, kawai na zo ne don in sanarwa shugaban kasa ziyarar da zamu kawo da ni da shugaban kamfanin Microsoft, Bill Gates a ranar Litinin mai zuwa.

Duk da Dangote bai bayyana dalilin ziyarar ba, amma bai rasa nasaba da shawarwari da Tinubu ke yi da masu ruwa da tsaki na gida da na waje.

Tinubu yana karban bakoncin masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci

A ranar 8 ga watan Yuni, jaridar Punch ta tattaro cewa Shugaba Tinubu ya karbi bakoncin manyan masu ruwa da tsaki na kamfanin Exxol Mobil.

Bakin sun hada da Liam Mallon da Richard Laing da kuma Mrs Adesua Dozie a wata ganawar sirri a fadar shugaban kasan.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Tinubu Ya Karbi Bakuncin Mai Kudin Afrika, Aliko Dangote a Aso Rock

Idan ba a mantaba, a ranar karbar rantsuwar kama mulki na Shugaba Tinubu ya yi alkawarin kawo karshen matsalolin masu zuba jari a kasar, cewar rahotanni.

Matsalolin wanda ya ce sun hada yawan haraji da kuma dokokin gwamnati da dama da suke kawo cikas ga masu zuba jari na gida da waje.

Yadda Tinubu Ya Karbi Bakuncin Dangote a Aso Rock

A wani labarin, Shugaba Tinubu a yau Juma'a ya karbi bakoncin Alhaji Aliko Dangote a fadarsa.

Shugaba Tinubu da Dangote sun yi kus-kus amma babu wani bayani da ya bulla a tsakaninsu.

Sai dai bayan ganawar ta su ta sirri, Aliko Dangote ya fadawa 'yan jaridu cewa ya zo ne kawai kan ziyararsu a ranar Litinin da Bill Gates.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.