Gwamna Radda Ya Jagoranci Gwamnonun Arewa Sun Gana da Tinubu a Villa
- Gwamnonin Arewa maso Yamma sun gana da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kan batun tsaro da noma a yankunansu
- Karkashin jagorancin gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, gwamnonin sun faɗa wa Tinubu matakan da suke ɗauka don zaman lafiya ya dawo
- Shugaban kasa ya tabbatar musu da cewa zai yi duk mai yuwuwa da haɗin kansu don tabbatar da zaman lafiya ya dawo a ƙasa baki ɗaya
FCT Abuja - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya jagoranci takwarorinsa gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma sun gana da shugaban ƙasa, Bola Tinubu, a Villa.
Vanguard ta ruwaito cewa gwamnonin sun zauna da Tinubu ne kan harkokin tsaro, noma da wasu batutuwa da suka shafi ƙasa baki ɗaya.
Gwamna Raɗɗa, shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma, ya ja takwarorinsa na jihohin Kano, Kaduna, Sakkwato, Zamfara, Kebbi da Jigawa zuwa fadar shugaban kasa.
Sakataren watsa labarai na gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wane abu suka tattauna yayin ganawa da Tinubu?
Sanarwan ta ce taron gwamnonin da shugaban kasa ya maida hankali ne kan matakan da suka tsara a ƙasa domin magance matsalar tsaro a shiyyarsu.
Arewa Maso Yamma na fama da kalubalen tsaro musamman ayyukan yan bindiga, gwamnonin suna faɗa wa Tinubu shirinsu na ganin matsalar ta zama tarihi.
Kazalika sun gaya Tinubu cewa Arewa maso Yamma ta shahara da noma, amma yanzu komai ya dogara da tsaro saboda sai akwai natsuwa manoma ke iya zuwa gona
Zamu goyi bayanku a kokarin dawo da tsaro - Tinubu
Da yake maida masu martani, shugaba Tinubu ya ce ba gudu ba ja da baya, zai taimaka wa gwamnonin a yunkurinsu na samar da tsaro tsakanin al'umma.
Ya ƙara nanata musu cewa noma na cikin abubuwa da gwamnatinsa zata ba fifiko domin burinsa Najeriya ta dogara da kanta a ɓangaren abinci.
Haka nan kuma, shugaban ya faɗa musu cewa cewa zai haɗa hannu da su wajen rage wa jama'a raɗaɗin cire tallafin man Fetur, kamar yadda Daily Post ta rahoto.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa gwamnonin Arewa maso Yamma ne na farko da suka fara zuwa wurin Tinubu kan batun tsaro da noma tunda ya hau mulki.
Sabon Dan Majalisa Ya Samu Nasarar Zama Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Imo
A wani rahoton kuma Sabon mamba ɗan shekara 40 a duniya ya zama kakakin majalisar dokokin jihar Imo ranar Jumu'a, 16 ga watan Yuni, 2023.
Honorabul Olemgbe, sabon ɗan majalisa a karon farko wanda zai wakilci mazaɓar Ihitte/Uboma, ya yi nasarar zama sabon kakaki ba tare da hamayya.
Asali: Legit.ng