Sojoji Ke Daukar Nauyin Satar Danyen Mai a Najeriya, Asari Dakubo Ya Tona Asiri

Sojoji Ke Daukar Nauyin Satar Danyen Mai a Najeriya, Asari Dakubo Ya Tona Asiri

  • Tsohon ɗan fafutukar neman sauyi a yankin Neja Delta, Asari Dakubo, ya fallasa masu hannu a satar ɗanyen mai a Najeriya
  • Jim kaɗan bayan ganawa da shugaban kasa Tinubu, Dakubo ya ce ƙaso 99 na ɓarayin mai suna da alaƙa da Sojojin Najeriya
  • Ya sha alwashin cewa zai taimakawa gwamnatin Tinubu wajen dawo da satar mai sufuli a yankuna masu albarkatun fetur

FCT Abuja - Fitaccen jagora a yankin Neja Delta kuma tsohon ɗan tawayen neman sauyi, Mujahid Asari Dakubo, ya tona asirin manyan ɓarayin ɗanyen mai a Najeriya.

Dakubo ya ce duk wannan Kes ɗin da ake fama na yawaitar satar mai a shiyya mai albarkatun man fetur, idan aka bi diddigi za'a gano Sojojin ƙasa da na ruwa ne ke ɗaukar nauyi.

Asari Dakubo da Bola Tinubu.
Sojoji Ke Daukar Nauyin Satar Danyen Mai a Najeriya, Asari Dakubo Ya Tona Asiri Hoto: Channelstv
Asali: UGC

Punch ta rahoto cewa Mista Dakubo ya yi wannan furuci ne yayin zantawa da yan jaridan gidan gwamnati jim kaɗan bayan ganawa da shugaba Tinubu cikin sirri a Villa, Abuja.

Kara karanta wannan

Tazarce Karo Na Uku: Obasanjo Ya Bayyana Masu Son Ya Yi Tazarce, Ya Bayyana Dalilansu

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sojoji ne tushen satar ɗanyen mai kuma ya zama wajibi mu yi wa 'yan Najeriya bayanin cewa kaso 99 cikin 100 na ɓarayin mai duk sojojin Najeriya ne musamman sojojin kasa da na ruwa."

Ya kuma jaddada goyon bayansa ga shirin gwamnatin tarayya na kawo karshen sace-sacen ɗanyen mai, kana ya nuna yaƙinin cewa gwamnatin Tinubu zata zakulo masu hannu a cikin Sojoji.

Wane batutun suka tattauna yayin ganawarsa da Tinubu?

Mista Dakubo ya bayyana cewa batun da ya shafi ɓarayin man fetur da kuma tsaro ne suka mamaye tsawon awanni biyu suna tattaunawa da shugaban kasa a Villa.

Ya nanata cewa a zaman ya tabbatarwa sabuwar gwamnati karkashin Tinubu cewa zai ba ta goyon baya 100 bisa 100 domin tabbatar da satar mai ta zama tarihi a Neja Delta.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu Ya Shiga Ganawar Sirri da Asari Dakubo a Aso Villa, Bayanai Sun Fito

A rahoton Vanguard, Dakubo ya ƙara da cewa:

"Ni da 'yan uwana mun tabbatarwa shugaban ƙasa cewa za'a kawo karshen satar mai da kuma fasa bututu a yankin Neja Delta. Zamu haɗa hannu da NNPCL domin ganin wannan ɗanyen aiki ya dawo Sufuli."

"Kada Ka Sake Shi": Asari Dokubo Ya Fada Ma Tinubu Hatsarin Da Ke Tattare Da Sakin Nnamdi Kano

A wani rahoton da muka kawo muku kuma kun ji cewa Dakubo ya shawarcu Tinubu kar ya yi kuskuren sako shugaban yan aware IPOB, Nnamdi Kanu.

Ya ce sakin shugaban masu fafutukar kafa kasar Biyafaran zai sake tada zaune tsaye ne a kasar don haka a barshi ya fuskanci shari'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262