Matashi Ya Jefa Kansa Cikin Gagarumar Matsala Don Rubutu Da Ya Yi Kan Kabilar Ibo A Tuwita
- Wani matashi da aka bayyana sunansa da Kehinde Adesogba Adekusibe, ya faɗa komar jami'an hukumar ‘yan sanda saboda rubutun da ya yi a soshiyal midiya
- Rundunar ‘yan sandan jihar Osun, ta kama matashin mai shekaru 28 mai amfani da kafafen sada zumunta na yanar gizo, kan wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Tuwita
- Olumuyiwa Adejobi, mai magana da yawun rundunar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Tuwita ranar Juma’a, 16 ga watan Yuni
Osun - Rundunar ‘yan sandan jihar Osun, ta sanar da kama wani matashi mai suna Kehinde Adesogba Adekusibe, ɗan kimanin shekaru 28, a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar 'yan sandan na Osun, Olumuyiwa Adejobi, shi ne ya tabbatar da kama Adekusibe a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, wacce Legit.ng Hausa ta ci karo da ita a safiyar Juma’a, 16 ga watan Yuni.
Dalilin da ya sa aka kama Adekusibe, ‘yan sandan sun yi bayani
Adejobi ya bayyana cewa, Adekusibe ya faɗa komar ‘yan sandan ne saboda saɓa ƙa’idar amfani da kafar sada zumunta da ya yi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Adejobi ya ƙara da cewa, wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Kamar yadda Adejobi ya wallafa:
“Sanarwar hukumar 'yan sanda jihar Osun - 15/06/2023
‘’’Yan sandan jihar Osun sun kama wani mai amfani da kafar sada zumunta da ya rubuta ‘A kashe ƙabilar inyamurai’.”
"A yau 15 ga watan Yuni, 2023, rundunar 'yan sandan jihar Osun ta kama wani Kehinde Adesogba Adekusibe 'namiji' mai shekaru 28 da ya saɓa ƙa'idojin amfani da kafar sada zumunta."
Karanta cikakken rubutun da ya jefa matashin cikin matsala daga shafin 'yan sanda a ƙasa:
Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna APC Ba Shi Da Lafiya, Ya Miƙa Mulki Ga Mataimakinsa Ya Tafi Ƙasar Waje Ganin Likita
‘Yan sanda sun kama wasu mutane 2 da ake zargi da laifin kisa, da ƙona ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka a Anambra
A wani labarin na daban kuma, rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajen kashe tare da ƙona ofishin jakadancin Amurka da ke ƙaramar hukumar Ogbaru ta jihar, a ranar Talata, 16 ga watan Mayu.
A wani bincike da hukumar ‘yan sandan ta gudanar, ta bayyana cewa an kashe mutane bakwai ne a harin.
Uku daga cikin bakwai ɗin da aka kashe, jami'an ofishin jakadancin Amurka ne, a yayin da sauran huɗun suka kasance 'yan sandan tafi da gidanka.
An kama Farfesa da yaransa saboda badaƙalar maƙudan kuɗaɗe
Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Mai Zaman Kanta (ICPC), ta kama tsohon shugaban Hukumar Jarabawar Share Fagen Shiga Manyan Makarantu (JAMB), Farfesa Dibu Ojerinde, kan badaƙalar kuɗaɗe masu tarin yawa.
Hukumar ta gurfanar da Farfesan tare da 'yan'yansa huɗu da wasu mutane da aka samesu da aikata laifin tare a gaban kotu.
Asali: Legit.ng