Ina Nan: Ban Tsere daga Najeriya saboda Tsoron Tinubu Ya Cafke Ni Ba - Ministan Buhari

Ina Nan: Ban Tsere daga Najeriya saboda Tsoron Tinubu Ya Cafke Ni Ba - Ministan Buhari

  • Tsohon Ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami ya karyata rade-radin cewa ya bar Najeriya
  • Rade-radin sun zagaye gari da sunan EFCC ta na binciken Lauyan, amma tuni ya karyata hakan
  • Malami ne babban lauyan gwamnati tun 2015 har zuwa lokacin da aa canza shugaban kasa

Abuja - Tsohon Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnati, Abubakar Malami, ya musanya zargin cewa ya tsere saboda zargin rashin gaskiya.

Ana rade-radin cewa tsohon Ministan shari’an ya fice daga Najeriya, Daily Trust ta rahoto Abubakar Malami SAN ya na mai karyata wannan labari.

Jita-jitar tayi kamari bayan Mai girma shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin a dakatar da shugaban hukumar EFCC, Mr. Abdulrasheed Bawa.

Ministan Buhari
Abubakar Malami da Muhammadu Buhari a UAE Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Abubakar Malami wanda mutumin Kebbi ne ya rike matsayin Lauyan gwamnatin tarayya na tsawon shekaru takwas a mulkin Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Nada Masu Bada Shawara, ‘Yan APC Sun Fara Hangen Kujerun Ministoci

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ana tunanin Malami ne ya shiga ya fita har Abdulrasheed Bawa ya samu shugabancin EFCC. Zargin da ya karyata tun ya na kan kujerar AGF.

Akwai zargi a kan Malami

Tribune ta fito da rahoto cewa za a so Malami ya yi bayani a kan zargin da ake yi na bacewar wasu Dala biliyan 2.4 da aka samu daga cinikin danyen mai.

Bayan haka akwai wasu zargin da ake tunani gwamnatin Najeriya za ta jefi tsohon Ministan da shi, saboda haka hukumar EFCC za tayi bincike a kan shi.

Da ya zanta da Daily Trust a ranar Alhamis, masanin shari’an ya ce hukumar EFCC ba ta gayyace shi ba, kuma bai tsere daga kasar kamar yadda ake fada ba.

“Ina nan a Najeriya kuma zan halarci daurin aure a masallacin Sheikh Isiyaka Rabi’u a Kano da karfe 2:30 na rana a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Tsohon Sanatan PDP Ya Zama Babban Mai Yabon Gwamnatin Tinubu Dare da Rana

EFCC ko wata hukuma ba ta kira ni ba. Zan mika kai na ga Najeriya da hukumomin ta idan da bukata.”
Ba ni da dalilin barin Najeriya kuma zan amsa goron gayyatar duk wata hukumar gwamnati da ta neme ni. Ni cikakken ‘dan kasa ne.

- Abubakar Malami SAN

Hadi Sirika ya na hannu?

A baya an ji labari cewa tsohon Ministan harkokin sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya je hannun Hukumar EFCC, ana bincike a kan shi bayan barin ofis.

Sanata Hadi Sirika ya musanya wadannan rade-radi ya ce jami’an EFCC ba su gayyace shi da nufin yin bayanin a game da kafa jirgin Nigeria Air ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng