Yan Boko Haram Sun Yi Wa Mutane 15 Yankan Rago a Jihar Borno
- Akalla mutane 15 ne aka yi wa yankan rago yayin da yan ta'addan Boko Haram suka kai hari kan al'umma a jihar Borno
- Tsagerun yan ta'addan sun farmaki kauyen Kofa a karamar hukumar Jere ta jihar a daren Alhamis har zuwa wayewar garin Juma'a
- Sun kuma farmaki al'ummar Molai Kura da Molai Gana inda suka yi wasu yankan rago
Borno - Wasu da ake zaton yan ta'addan Boko Haram ne sun yi wa akalla mutane 15 yankan rago a wasu hare-hare da suka kai kan garuruwa biyu a karamar hukumar Jere ta jihar Borno.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa maharan sun farmaki kauyen Kofa da tsakar dare sannan suka fara harbi kan mai uwa da wahabi, wanda ya shafe kimanin awa daya zuwa safiyar Juma'a.
An tattaro cewa sun kuma farmaki Molai Kura da Molai Gana inda suka yi wa wasu mutane yankan rago.
An kuma rahoto cewa mazauna yankin da dama sun tsere daga gidajensu domin samun mafaka a dazazzukan da ke kusa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yan Boko Haram sun farmaki manoma a gonakinsu, sun yi masu yankan rago
Wani babban dan kungiyar yan banga, Bukar Ali Musty, ya ce an kai harin ne yayin da manoma ke aiki a gonakinsu a karamar hukumar Jere.
A cewarsa, manoman na tsaka da aiki a gonakinsu a kusa da Molai, wajen garin Maduguri a ranar Alhamis lokacin da yan ta'addan suka far masu sannan suka yanke masu kawuna.
Ya ce:
"A kalla gawarwaki 15 aka kwashe a safiyar nan, hare-haren ya gudana a jiya (Alhamis).
"Manoma bakwai aka fillewa kai yayin da suke aiki a gonakinsu kuma maharan sun yanka wuyan mutane takwas a gidajensu."
Ya zama dole manyan gari su farka don yi wa tufkar hanci, Dan JTF
Wani dan sa kai na JTF wanda ya kasance cikin tawagar da suka kwashe mutanen, ya nuna damuwa kan hare-haren, yana mai cewa ya zama dole dukkan masu ruwa da tsaki su farka don ganin lamarin bai ci gaba ba.
Majiyar ta ce:
"Abun bakin ciki ne duba ga nasarar da muka samu a yan watannin nan ba tare da hare-hare kan garuruwa ba.
"Ina wajen da safen nan. Ina mamakin ganin an yi wa mutum kamar ni yankan rago. Gaba daya gawarwakin da muka samo mun gansu ne kwance cikin jiki kuma ina ganin akwai bukatar mu tashi tsaye a kan wannan makiyan zaman lafiyan."
Sojoji sun yi gagarumin nasara kan Boko haram, sun kwato kudade
A wani labari na daban, mun ji cewa sojojin Najeriya sun sanar da ƙwace sama da naira miliyan 11, sannan kuma sun halaka tare da kame ‘yan ta’adda da dama a hare-haren da suka kai.
Sojojin sun kuma ƙwace makamai a samamen da suka kai a kauyuka, maboya, sansanoni da wuraren atisaye a ƙauyuka, tsaunuka da bakin ruwa a jihohin Borno, Adamawa da Yobe cikin makonni biyu da suka gabata.
Asali: Legit.ng