Matashi Ya Bakunci Lahira Yayin Da Ya Shiga Tiransifoma Da Nufin Satar Wayoyi A Kogi
- Wutar lantarki ta yi ajalin wani matashi mai suna Olukuluku Kabiru yayin da ya shiga cikin babban injin rarraba wuta (tiransifoma) don satar kayayyakin cikinta
- Manajan kamfanin AEDC, Michael Eneromi ya bayyana cewa sun samu rahoton mutuwar matashin, inda ya koka kan yadda lamarin ke kara yawa
- Jami'an tsaro da ma'aikatan kamfanin sun dauki gawar mamacin zuwa asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Lokaja babban birnin jihar Kogi
Kogi - Wayoyin lantarki sun yi ajalin wani matashi mai suna Olukuluku Kabiru yayin da yake kokarin satar manyan wayoyin cikin injin bada wutar lantarki ta Kamfanin Wutar Lantarki na Abuja (AEDC).
Lamarin ya faru ne a wani sashi na wutar lantarkin kamfanin da ke hanyar Camp cikin Lokoja babban birnin jihar Kogi.
Manajan kamfanin wutar, Michael Eneromi ya ce an ba su rahoton bayan samun gawar mamacin a kusa da wurin, inda ya ce wannar injin ba da wutar ba yau aka fara kai mata farmaki ba, cewar Punch.
Ya bayyana irin yawan satar da ake yi a tiransifoman
A cewarsa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"A makon da ya gabata, mun gyara wannan babban injin rarraba wutar lantarki din bayan mutanen yankin sun kawo korafin cewa an sace kayan ciki.
"A jiya ma mun gyara wannan injin saboda satar da aka yi a cikinta, mun tura sako muna neman N1.9m don gyara ta."
Eneromi ya ce ana yawan zargin ma'aikatansu da satar kayan tiransifoma
Eneromi ya ce mutuwar wannan mutumin ya cire ma'aikatansu daga zargin cewa su suke satar wayoyi cikin babban injin rarraba wutar lantarki.
Ya kara da cewa:
"Shekaruna 20 ina aiki a wannan kamfani na NEPA da AEDC, ba a taba samun wani daga cikin ma'aikatanmu ya saci kayan cikin babban injin rarraba wutar lantarki ba.
"Na ji dadi cewa yanzu mutanen Lokoja za su fahimci cewa wasu bata gari ne ke satar.
"Ina son na roki mutane cewa su dauki kayan wutar lantarki kamar nasu, kuma ina kira ga 'yan sakai da sauran jami'an tsaro da su saka ido sosai.
"Tare da sanar da ma'aikatanmu idan akwai wani matsala da suka fahimta, su tabbatar jami'anmu ne kadai masu dauke da katin shaidan aiki suke shiga don gyara wata matsala."
Tuni jami'an tsaro da ma'aikatan AEDC suka dauki gawar mamacin zuwa asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Lokoja, Daily Post ta tattaro.
Unguwar Kurmin Kogi Sun Koka Kan Rashin Wuta Na Tsawon Shekaru 8 a Kaduna
A wani labarin, mazauna Unguwar Kurmin Kogi a karamar hukumar Ikara sun koka kan rashin wuta.
Mazauna yankin sun koka cewa sun shekara akalla takwas ba tare da sun ga kyallowar wutar lantarki ba.
Hakan ya fara ne tun shekarar 2015 bayan an tafka ruwa kamar da bakin kwarya a yankin.
Asali: Legit.ng