Biyu Babu: Bakano Ya Yi Karyar Garkuwa Da Kansa, Barayi Sun Sace N356k Da Ya Karba Na Fansa

Biyu Babu: Bakano Ya Yi Karyar Garkuwa Da Kansa, Barayi Sun Sace N356k Da Ya Karba Na Fansa

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi dan shekara 19 mai suna Nafi'u Suleiman bisa zargin garkuwa da kansa
  • Nafi'u ya tabbatar wa 'yan sanda cewa shi kadai ya kitsa wannan mummunan aika-aika don samun kudi daga kawunsa
  • Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mohammed Usaini Gumel ya tabbatar da kama matashin inda ya ce an kama shi ne yayin da ake bincike

Jihar Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wani matashi mai suna Nafi'u Suleiman bisa zargin garkuwa da kansa tare da karban kudin fansa N365,000.

Wanda ake zargin ya karbi kudin fansar ne daga wurin kawunsa wanda kuma yana aiki a karkashinsa a kauyen Garindau da ke karamar hukumar Warawa cikin jihar Kano.

'Yan sanda sun cafke matashin da ya yi garkuwa da kansa
Matashi Ya Yi Garkuwa Da Kansa A Jihar Kano. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Da yake bayani a gaban 'yan sanda, Nafi'u ya ce ya yi garkuwa da kansa ne don ya sayi kayan sakawa da sauran abubuwa na rayuwa, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

La'adar N200k: Yan Sandan Najeriya Na Neman Wani Mutum Ruwa A Jallo Osun Kan Mallakar Bindigu

Matashin ya bayyana yadda ya yi garkuwa da kansa

Ya kara da cewa yaje wani gida da ba a kammala ba, ya shafe kwanaki a can, yayin da ya ce daga bisani kuma aka sace kudin fansar da ya karba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"Ni na kitsa komai, nayi amfani da wani layin waya na kira mai gidana wanda kuma shi ne kawuna, na bukaci kudin fansa da inda za su ajiye kudin idan sun kawo.
"Duk lokacin da nake bukatan abinci nakan fito na siya kuma na koma maboyata.
"Amma ban yi amfani da ko kashi 1 na kudin ba, N20,000 kawai na kashe na binne sauran a wani wuri, lokacin da na koma don daukar kudin sai na samu an sace."

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mohammed Usaini Gumel ya ce an kama wanda ake zargin lokacin bincike, yayin da ya tabbatar da cewa shi kadai ya kitsa hakan don samun kudi a wurin kawunsa, cewar rahotanni.

Kara karanta wannan

Yan Gidan Magajiya Sun Harzuka Sun Maka Kwastoma A Kotu Kan Tura Musu Alat Na Bogi Bayan Sun Gama Harka

’Yan Sanda Sun Kwamushe Bakin Haure 12 Daga Kasashen Ketare, Wadanda Saudiyya Ta Koro

A wani labarin, Rundunar 'yan sandan jihar Kano sun cafke wasu bakin haure 12 a jihar.

Hukumar ta ce bakin hauren 'yan kasashen ketare ne da Saudiyya ta koro su kasashensu.

Bakin hauren wadanda 'yan kasashen Mali da Niger ne, an kamasu a wani otal da ke birnin Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.