Cin Amanar Kasa: ICPC Ta Kama Farfesa Da ’Ya’yansa 4 Bisa Zargin Bindige Makudan Kudade
- Hukumar ICPC ta gurfanar da tsohon makatakardan Hukumar JAMB a gaban kotu bisa zargin rashawa da badakalar kudade
- Wanda ake zargin, Farfesa Dibu Ojerinde an gurfanar da shi a gaban babbar kotun Tarayya da ke Abuja da wasu 'ya'yansa guda hudu
- Alkalin kotun ya ba da belin 'ya'yan Farfesan akan kudi N20m kowannensu tare da kawo mai daukar belin da ke da kadara makamancin kudin
FCT, Abuja - Hukumar ICPC ta gurfanar da tsohon magatakardar Hukumar Jarrabawar Sharar Fage ta JAMB, Dibu Ojerinde bisa zargin badakalar makudan kudade.
Farfesa Ojerinde an gurfanar da shi ne a gaban kotun Tarayya da ke Abuja da 'ya'yansa guda hudu da sauransu.
Daga cikin 'ya'yan nasa hudu akwai Olumide Ojerinde da Mary Ojerinde da Oluwaseun Ojerinde da kuma Adebayo Ojerinde, Premium Times ta tattaro.
Daga cikin sauran wadanda ake zargi akwai kamfanoni guda biyar da makaranta guda daya wadanda dukkansu ana zarginsu da hannu dumu-dumu a badakalar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ICPC ta ce Farfesan ya sabawa dokar kasa
Hukumar ta ICPC ta bayyana irin badakalar da Mista Ojerinde ya yi, inda ta ce hakan ya sabawa doka.
Dukkan wadanda ake zargin sun musanta aikata laifukan da ake tuhumarsu akai.
Alkalin kotun, Inyang Ekwo ya ba da belin Mista Ojerinde kamar yadda babbar kotun Tarayya a Abuja ta ba shi a farko.
'Ya'yan Farfesan za su biya kudin beli N20m ko wannensu
Yayin da dukkan 'ya'yan nasa aka bada belin kowannensu akan kudi har N20m, sannan wadanda za su karbi belin nasu dole su mallaki kadara da bata yi kasa da kudin belin ba.
Alkalin kotun har ila yau ya umarci sauran wadanda ake zargin da su kawo fasfot nasu, da sharadin ba za su bar kasar ba sai da izinin kotu.
Daga bisani Alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraran karar har zuwa 13 da 14 da 15 da kuma 16 ga watan Nuwamba.
ICPC Ta Bankado Sabbin Naira Da Aka Boye a Durowan Banki
A wani labarin, Hukumar ICPC ta bayyana yadda ta bankado makudan kudade a wani banki.
Hukumar ta ce an boye makudan kudaden ne a durowan wani banki a cikin kasar nan.
A wani faifan bidiyon da hukumar ta wallafa an gano ana umartar jami'an bankin da su bude durowan kudin.
Asali: Legit.ng