Sojoji Sun Aika Yan Ta'adda 42 Lahira, Sun Cafke Wasu 96 A Arewacin Najeriya
- Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa a cikin makwanni biyu da suka gabata ta hallaka akalla 'yan bindiga 42 da sauran masu tada zaune tsaye
- Daraktan yada labarai na rundunar, Musa Danmadami ya ce rundunar ta kuma hallaka 'yan Boko Haram da dama a yankuna daban-daban
- Ya kara da cewa jami'ansu sun kuma kama wadanda ake zargi 13 a kauyen Irekpeni akan hanyar Lokoja-Kabba-Okene da ke jihar Kogi
FCT, Abuja - A cikin makwani biyu da suka gabata, rundunar sojin Najeriya ta hallaka akalla 'yan bindiga 42 da 'yan Boko Haram da sauran masu tada tsaune tsaye.
Daraktan yada labarai na hukumar, Musa Danmadami shi ya bayyana haka a ranar Alhamis 15 ga watan Yuni a Abuja.
Danmadami ya ce rundunar ta kama wadansu da ake zargi guda 13 a kauyen Irekpeni akan hanyar Lokoja-Kabba-Okene da ke jihar Kogi.
Yan Gidan Magajiya Sun Harzuka Sun Maka Kwastoma A Kotu Kan Tura Musu Alat Na Bogi Bayan Sun Gama Harka
Rundunar ta kama 'yan kungiyar ISWAP da wasu tsagera da dama
Ya ce jami'ansu sun samu wayoyin hannu da ke dauke da lambar wayoyin 'yan kungiyar ISWAP wadanda jami'an tsaro ke nema, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa an kama masu garkuwa da mutane 7 da wadanda suke mara musu baya da kuma masu ba su bayanan sirri a karamar hukumar Nasarawa Eggon da ke jihar Nasarawa.
Har ila yau, ya ce rundunar ta kama masu laifuka daban-daban 86 tare da ceto wasu da aka sace a shiyyoyi biyu na kasar.
A shiyyar Arewa maso Yamma, Danmadami ya ce jami'an Hadarin Daji sun hallaka 'yan fashi 38 tare da kama 10 bayan ceto wasu mutane guda 24 daga hannun masu garkuwa.
Rundunar Sojin ta samu muggan makamai a hannun tsageran
Daily Nigerian ta tattaro cewa rundunar ta samu muggan makamai a hannun wadanda aka kaman da suka hada da AK-47 guda 20 da harsashensu dauri 28 da abubuwa masu fashewa da sauran bindigogi masu hatsari.
A cewarsa:
"Sauran kayayyakin da aka samu sun hada da babura 19 da wayoyi 10 da radiyo guda 3 da kuma shanu 34.
"Tsakanin 2 ga watan Yuni zuwa 6 ga watan Yuni rundunar ta kai samame maboyar shugaban 'yan ta'adda karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
Sojoji Sun Gano Wani Makeken Rami Make Da Makamai Masu Dimbin Yawa A Sambisa
A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta samu wani tafkeken rami cike da makamai a jihar Borno.
Rundunar Operation Hadin Kai ta yi nasarar gano ramin bayan kai wani samame a yankin.
Samamen ai kai shi a yankin Ukuba da ke karamar hukumar Bama a ranar Asabar 13 ga watan Mayu.
Asali: Legit.ng