Abdulsamad Rabiu Ya Rasa Sama Da N1trn a Dukiyarsa Cikin 'Yan Sa'o'i, Ya Yo Kasa a Jerin Attajiran Duniya
- A cikin ƴan sa'o'i kaɗan attajiri na biyu wanda ya fi kowa kuɗi a Najeriya, Abdulsamad Rabiu, ya rasa sama da N1trn
- Hakan ya faru ne bayan babban bankin Najeriya ya bayar da umarnin haɗe farashin da ake canjin dala zuwa naira ya zama guda ɗaya
- Rasa dukiyar da Abdulsamad ya yi ya sanya ya yi ƙasa daga matsayin da yake a kai a cikin jerin attajiran duniya, inda ya yi ƙasa da mataki 200 a jerin
Abdulsamad Rabiu, shugaban rukunin kamfanonin BUA, ya yi rashin dukiya mai tarin yawa bayan darajar naira ta faɗi ƙasa warwas.
Legit.ng ta rahoto cewa babban bankin Najeriya ya bayar da sanarwar cewa yanzu kasuwa ce za ta riƙa yanke yadda za a riƙa canjin naira zuwa dala.
Babban bankin ya kuma bayar da umarni ga bankuna cewa su siyar da dala ba tare da wani shamaki ba.
A cikin ƴan sa'o'i kaɗan, darajar naira ta faɗi ƙasa warwas inda ta koma N791/$1 daga fara farashin da aka fara siyar da ita a ranar na N461/$1.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yadda dukiyar Rabiu ta yi ƙasa
Bloomberg ta rahoto cewa dukiyar Abdulsamad Rabiu, ta yo ƙasa daga $8.27bn a ranar Talata, 13 ga watan Yuni 2023, zuwa $5.54bn a ƙarshen ranar Laraba, 14 ga watan Yunin 2023.
Hakan na nufin cewa a cikin sa'o'i 24 ya rasa sama da N1.2trn ($2.73bn) daga cikin dukiyarsa.
Haka kuma, Abdulsamad ya yo ƙasa da mataki 200 a cikin jerin attajiran duniya inda a ranar Laraba, ya koma matsayi na 463 cikin jerin attajiran duniya saɓanin matsayi na 263 da yake a ranar Talata
Meyasa faɗuwar naira ta shafi Abdulsamad Rabiu?
Ranar Dimokuradiyya: Dalilai 5 Da Suka Sa Ranar 12 Ga Watan Yuni Ke Da Muhimmanci A Tarihin Najeriya
Abdulsamad yana daga cikin ƴan Najeriya masu zuba hannun jari da yawa a ƙasar inda ya mayar da hankali wajen kayayyakin masarufi na amfanin yau da kullum.
Mafi yawa daga cikin kayayyakin da Abdulsamad yake samarwa ana cinikinsu ne da naira.
Kamfanin simintin BUA, shi ne kamfani mafi girma na biyu a Najeriya, yayin da kamfanin BUA Foods, shi ne na ɗaya wajen samar da taliya da fulawa a ƙasar.
Arzikin Dangote Ya Yi Tashin Gwauron Zabi
A wani labarin, attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiƴar Afirika, Aliko Dangote, ya ƙara samun tagomashi a dukiyarsa.
A cikin ƴan sa'o'i kaɗan arziƙim Dangote ya ƙaru da sama da $769m, wanda hakan ya sanya ya ƙara sama a cikin jerin attajiran duniya.
Asali: Legit.ng