Kotu Ta Yi Fatali Da Karar Da El-Rufai Ya Shigar Kan Shehu Sani

Kotu Ta Yi Fatali Da Karar Da El-Rufai Ya Shigar Kan Shehu Sani

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai ya yi rashin nasara akan ƙarar da ya shigar da Sanata Shehu Sani
  • El-Rufai ya maka Shehu Sani a gaban kotu kan zargin ɓata masa suna inda ya buƙaci kotun ta sanya ya biya shi diyya
  • Sai dai, alƙalin kotun ya yi fatali da ƙarar da El-Rufai ya shigar a gabanta bayan ya hango wani kuskure da aka tafka a ƙarar

Jihar Kaduna - Wata babbar kotu a jihar Kaduna ta yi fatali da ƙarar ɓata suna da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar akan Sanata Shehu Sani, tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya.

El-Rufai ya buƙaci da tsohon Sanatan ya biya shi diyyar N2bn, kan wasu kalamai da ya yi a kansa.

Kotu ta yi fatali da karar El-Rufai kan Shehu Sani
Kotun ta yi fatali da ƙarar da El-Rufai ya shigar Hoto: Shehu Sani, Nasir Ahmed El-Rufai
Source: Facebook

A cikin ƙarar wacce aka shigar a shekarar 2018, tsohon gwamnan ya ce Shehu Sani ya ɓata masa suna inda ya jefe shi da munanan kalamai.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da Ya Kamata ku sani Game da Akpabio, Sabon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya

El-Rufai ya yi iƙirarin cewa kalaman na Shehu Sani ƙarya ce tsagwaronta kuma sun taɓa masa ƙima a idon jama'a.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake yanke hukuncinsa a ranar Alhamis, alƙalin kotun mai shari'a H.A.L Balogun, ya bayyana cewa ƙarar cin mutuncin tsarin kotu ne, cewar rahoton The Cable.

Alƙalin ya bayyana dalilin fatali da ƙarar

Balogun ya bayyana cewa El-Rufai ya shigar da ƙarar a kotuna daban-daban a jihar, rahoton The Guardian ya tabbatar.

A lokacin da aka fara sauraron ƙarar, lauyan Shehu Sani, Kimi Livingstone Appah, ya tunatar da kotun cewa tsohon gwamnan ya shigar da irin ƙarar har a kotuna guda huɗu a jihar.

Alƙalin kotun ya amince da jayayyar sauraron ƙarar da lauyan ya yi, inda ya yi fatali da ƙarar.

Da yake magana da manema labarai bayan an yanke hukunci, Appah ya bayyana cewa hukuncin kotun nasara ce ga dimokuraɗiyya da ƴancin faɗar abinda mutum yake so.

Kara karanta wannan

Ranar Dimokuradiyya: Dalilai 5 Da Suka Sa Ranar 12 Ga Watan Yuni Ke Da Muhimmanci A Tarihin Najeriya

El-Rufai da Shehu Sani sun daɗe basa ga maciji tun bayan da dangantakar siyasa da ke a tsakaninsu ta yi tsami.

Shehu Sani Ya Yi Wa El-Rufai Tonon Silili

A wani labarin, tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya bayyana wani sirri na tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai.

Shehu Sani ya bayyana cewa tsohon gwamnan yana nan yana jiran samun wnai muƙami mai gwaɓi a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng