EFCC Ta Sanar da Sabon Shugaban Rikon Kwarya Bayan Tinubu Ya Dakatar da Bawa

EFCC Ta Sanar da Sabon Shugaban Rikon Kwarya Bayan Tinubu Ya Dakatar da Bawa

  • Abdulkarim Chukkol ya zama shugaban rikon kwarya a EFCC jim kadan da dakatar da Abdulrasheed Bawa
  • Sanarwa ta fito daga Wilson Uwujaren ya cewa an sanar da wanda zai canji Bawa a matakin rikon kwarya
  • Tun da aka kafa hukumar EFCC a tarihi, Chukkol ya na cikin wadanda su ka fara aiki, har ya kai Darekta

FCT, Abuja - A sakamakon dakatar da Abdulrasheed Bawa da mai girma shugaban kasa yayi, hukumar EFCC ta sanar da wanda zai maye gurbinsa.

Daily Trust ta tabbatar da cewa Abdulkarim Chukkol shi ne wanda zai maye gurbin Abdulrasheed Bawa har zuwa lokacin da za a nada cikakken shugaba.

Chukkol ya yi karatu a makarantar nan ta Quantico da ke horar da jami’ar hukumar FBI, sannan ya yi kwas a wata makarantar tsaro da ke kasar Jamus.

Kara karanta wannan

Abdulrasheed Bawa: Dalilai 2 Da Ake Zato Suka Sa Tinubu Dakatar Da Shugaban EFCC Daga Mukaminsa

EFCC.
Abdulkarim Chukkol zai rike EFCC Hoto: 9jaflaver.com
Asali: UGC

Sabon shugaban rikon kwaryan na EFCC ya je makarantar ilmin yake-yake ta Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Digiri zuwa fara aikin bincike

Tashar Channels ta ce Chukkol ya yi digirinsa ne a bangaren ilmin tattalin harkargona daga jami’ar Maiduguri (2000) sai ya samu satifiket a ketare.

Daga cikin takardun shaidarsa akwai satifiket a binciken masu laifi a shari’a daga jami’ar Virginia da babbar difloma a kan tsaro yanar gizo a Washington.

Jawabi daga bakin Kakakin EFCC

A wani jawabi da ya fitar a ranar Alhamis, mai magana da bakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya sanar da nadin sabon shugaban rikon kwaryon.

Sanarwar ta ce da Mista Chukkol aka kafa EFCC, su aka fara yi wa kwas, ya kuma kware musamman wajen binciken laifin yanar gizo da na satar kudi.

Rahoton ya ce a baya ya yi aiki a matsayin shugaban sashen binciken manya da laifuffukan yanar gizo a Legas da Abuja tsakanin shekarar 2011 da 2016.

Kara karanta wannan

Daga Ribadu Zuwa Olukoyede: Jerin Sunayen Shugabannin EFCC Da Jihohi/Yankunansu

Uwujaren ya ce Chukkol ya fara rike sashen hukumar da ke Uyo a 2017 da Fatakwal a 2020.

Alaka da kasashen ketare

A game da alaka da kasashen waje kuwa, sabon shugaban ya yi aiki da jami’arn FBI da ‘yan sandan kasashen Australiya, Jamus, Hollanda da Afrika ta Kudu.

Sabon shugaban ya yi kwas har a jami’ar Oxford a 2022 kuma ya yi hulda da kasashe kamar su Sifen, Beljium, Kanada, Birtaniya da Amurka da dai sauransu.

Naira ta na yawo a kasuwa

Naira ta yi mummunan faduwar da kusan ba a taba gani ba a karshen makon da ya wuce a Najeriya. Legit.ng Hausa ta kawo maku wannan rahoto a baya.

Labari ya canza daga baya Dalar Amurka ta fado daga N767 zuwa N754 a kasuwannin canjin kudi, kwatsam sai aka ji CBN ya fito da sabon tsari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel