Da Dumi-Dumi: IGP Ya Bayar Da Umarnin Kulle Sakatariyoyin Kananan Hukumomin Jihar Plateau

Da Dumi-Dumi: IGP Ya Bayar Da Umarnin Kulle Sakatariyoyin Kananan Hukumomin Jihar Plateau

  • Babban sufeta Janar na ƴan sandan ƙasar nan ya bayar da umarnin a rufe sakatariyoyin ƙananan hukumonin jihar Plateau
  • IGP Usman Baba ya bayar da umarnin ne biyo bayan taƙaddamar shugabanci da ake yi kan ƙananan hukumomin
  • Gwamnan jihar ya dakatar da shugaban ƙananan hukumomin inda suka tubure suka sha alwashin ƙin barin muƙamansu

Jihar Plateau - Babban sufeton ƴan sanda na ƙasa, Usman Baba ya bayar da umarnin kulle dukkanin sakatariyar ƙananan hukumomi 17 na jihar Plateau, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Plateau, Bartholomew Onyeka, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Alabo Alfred ya rattaɓawa hannu, cewar rahoton The Punch.

IGP ya bayar da umarnin rufe kananan hukumomin jihar Plateau
IGP Usman Baba Alkali Hoto: Intelregion.com
Asali: UGC

Sanarwar ta yi nuni da cewa an ɗauki wannan matakin ne domin guje wa yi wa doka karan tsaye biyo bayan hargitsin da ya tashi kan naɗin sabbin shugabanni a ƙananan hukumomin da gwamnan jihar, Caleb Mutfwang, ya yi.

Kara karanta wannan

Sanata Barau Jibrin: Muhimman Abubuwan Sani 5 Dangane Da Sabon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Babban sufeta janar na ƴan sanda, Usman Alkali Baba, ya umarci kwamishinan ƴan sanda jihar Plateau, CP Bartholomew Onyeka, da ya rufe dukkanin sakatariyoyin ƙananan hukumomi 17 na jihar."
"Hakan ya zama wajibi ne saboda hargitsin da ya tashi kan shugabancin ƙananan hukumomin da barazanar da magoya baya da shugabannin ƙananan hukumomin su ke yi kan kayan gwamnati da rayuwa da dukiyoyin al'ummar jihar."
"A dalilin hakan rundunar ƴan sandan jihar Plateau ba za ta zuba ido ta bari abubuwa su taɓarɓare ba, hakan ya sanya mu ka ɗauki wannan ƙwaƙƙwaran matakin na rufe sakatariyoyin ƙananan hukumomin."

Rundunar ƴan sandan ta kuma yi gargaɗin cewa ba za ta sassautawa duk wanda ya yi ƙoƙarin hana cika wannan umarnin ko kawo ruɗani a sakatariyoyin ƙananan hukumomin.

Yadda rikicin ya samo asali

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jibrin Barau Daga Kano Ya Zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa

A satin da ya gabata ne gwamnan jihar Caleb Mutfwang, ya dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin tare da kansilolinsu domin bayar da dama a gudanar da bincike kan zarge-zargen baɗaƙalar kuɗi da majalisar dokokin jihar take yi musu.

Daga baya gwamnan ya maye gurbinsu da shugabannin kwamitin riƙon ƙwarya amma tsaffin shugabannin waɗanda ƴan jam'iyyar APC, sun yi fatali da dakatarwar da aka yi musu inda suka sha alwashin ci gaba da zama a ofisoshinsu.

EFCC Ta Gayyaci Tsohon Ministan Buhari

A wani labarin na daban kuma, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), ta gayyaci tsohon ministan sufurin jiragen sama a gwamnatin shugaba Buhari.

EFCC ta gayyaci Hadi Sirika domin ya amsa mata tambayoyi kan ƙaddamar da jirgin saman Najeriya da ya yi kafin ya bar ofis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng