Emefiele Da Wani Babban Jami’in Gwamnati 1 Da Tinubu Ya Dakatar Cikin Makonni 2

Emefiele Da Wani Babban Jami’in Gwamnati 1 Da Tinubu Ya Dakatar Cikin Makonni 2

Shugaban kasar Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya fara aikin tsarkake jami'an gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Hakan ya kasance ne yayin da Tinubu ya dauki tsauraran matakai cikin makonni biyu da kama aiki a matsayin shugaban kasa, lamarin da ya shafi akalla manyan jami'an gwamnatin da ta shude guda biyu.

Shugaban kasa Bola Tinubu
Emefiele Da Wani Babban Jami’in Gwamnati 1 Da Tinubu Ya Dakatar Cikin Makonni 2 Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Shugaban kasar ya dakatar da wadannan manyan jami'ai daga ofis biyo bayan abun da ya bayyana a matsayin cin mutuncin kujerarsu da kuma tarin laifuffuka da suka shafi ayyukansu a ofis.

Jim kadan bayan dakatar da su, shugaban kasar ya bayar da umurnin bincikarsu sannan ya kuma nemi su mika mulki ga manyan jami'ai a hukumominsu.

Dakataccen gwamnan CBN, Godwin Emefiele
Emefiele Da Wani Babban Jami’in Gwamnati 1 Da Tinubu Ya Dakatar Cikin Makonni 2 Hoto: Central Bank of Nigeria
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. An dakatar da Godwin Emefiele daga mukaminsa a matsayin gwamnan CBN

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, Har Sai Baba-Ta-Gani

A ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni ne shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, daga ofis kuma ya fara aiki nan take.

Ofishin sakataren gwamnatin tarayya ne ya sanar da dakatarwa da aka yi masa.

Hakan ya kasance ne saboda binciken da ke gudana kan ofis dinsa da kuma shirin gyara bangaren hada-hadar kudi na tattalin arzikin kasar, kamar yadda daraktan labarai na ofishin SGF, Willie Bassey ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a.

Awanni bayan dakatar da Emefiele daga ofis, sai jami'an rundunar tsaro na farin kaya suka tsare shi.

An umurci Emefiele da ya gaggauta mika harkokin ofishinsa ga mataimakin gwamnan bankin wanda zai yi aiki a matsayin gwamnan CBN zuwa lokacin da za a kammala bincike da gyare-gyaren.

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, Emefiele ya shafe kwanaki biyar a tsare a hannun SSS.

Kara karanta wannan

Sai Na Ga Bayanku: Sabon Gwamnan APC a Arewa Ya Yi Babban Tanadin Karar Da ’Yan Bindiga

Dakataccen shugaban EFCC, AbdulRasheed Bawa
Emefiele Da Wani Babban Jami’in Gwamnati 1 Da Tinubu Ya Dakatar Cikin Makonni 2 Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

2. An dakatar da AbdulRasheed Bawa daga ofis a matsayin shugaban EFCC

A daren ranar Laraba, 14 ga watan Yuni, shugaban kasa Tinubu ya dakatar da AbdulRasheed Bawa, CON, daga matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) har sai baba-ta-gani saboda zarge-zargen da ake masa.

Ana dakatar da Bawa, sai Mohammed Umar Abba ya zama mukaddashin shugaban hukumar ta EFCC.

Awanni bayan nan, hukumar tsaron farin kaya ta gayyaci Bawa don ci gaba da amsa tambayoyi.

Muhimman abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da mukaddashin shugaban EFCC, Mohammed Abba

A gefe guda, mun ji cewa bayan dakatar da shi, an umurci Bawa da ya gaggauta mika harkokin ofishinsa ga daraktan ayyuka na hukumar, Mohammed Umar Abba, wanda zai jagoranci harkokin ofishin shugaban hukumar EFCC.

An haifi Mohammed Umar Abba a ranar 22 ga watan Yunin 1965 a karamar hukumar Tudunwada ta jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng