Tsohon Minista Ya Kai Kara Wajen EFCC, Ya Ce Tsohon Gwamna Ya Karkatar da N1tr

Tsohon Minista Ya Kai Kara Wajen EFCC, Ya Ce Tsohon Gwamna Ya Karkatar da N1tr

  • Edwin Clark ya na zargin Ifeanyi Okowa ya karkatar da N1tr da aka biya a matsayin 13% na kudin mai
  • Dattijon ya rubuta takarda zuwa ga Hukumar EFCC, ya na so a binciki tsohon Gwamnan na jihar Delta
  • Clark ya ce Okowa ya handame dukiyar al’umma a lokacin yana Gwamna, ba tare da ya yi wasu ayyuka ba

Delta - Edwin Clark wanda ya taba yin Minista a Najeriya, ya na tuhumar Dr. Ifeanyi Okowa da karkatar da kudi sama da Naira Tiriliyan daya.

Premium Times ta ce Edwin Clark ya na zargin Dr. Ifeanyi Okowa ya yi sama da fadi da kason jihohi masu arzikin fetur a lokacin yana Gwamna.

Tsohon Gwamna
Ifeanyi Okowa da Yemi Osinbajo ya na Gwamna Hoto: www.chronicle.ng
Asali: UGC

Shugaban kungiyar PANDEF ya ce su na zargin gwamnatin tarayya da satar dukiyarsu, ashe gwamnonin yankin su ke hana al’umma cigaba.

Kara karanta wannan

Emefiele Ya Jawo Aka Yi Mani Daurin Kwanaki 101 Saboda Fallasa Badakalar $3bn

Dattijon ya fadi haka a lokacin da aka gayyace shi gidan talabijin Arise a ranar Laraba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Nyesom Wike ya tona asiri

Gwamna Nyesom Wike ya fara fasa-kwai a Nuwamban 2022 cewa cewa gwamnatin tarayya ta biya jihohin da ke da arzikin fetur bashin hakkokinsu.

Bayan Wike ya yi wannan magana ne sai aka ji Garba Shehu yana cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta biya N296.63bn ga wadannan jihohi tara.

An rahoto Clark yana cewa a dalilin haka ne ya kalubalanci Ifeanyi Okowa, ya rubuta masa wasika domin ya yi bayanin inda ya kai kudin jihar Delta.

Ina aka kai kudin?

Dalilin da Okowa ya bada shi ne ya yi amfani da N5bn wajen biyan fansho, Clark ya ce bai yarda wadannan kudi su na cikin bashin 13% da aka biya ba.

Haka zalika an ce an yi amfani da kudin wajen gina jami’a a kauyen Okowa. Ganin bai gamsu da uzurin ba, dattijon ya yi hayar Lauya na musamman.

Kara karanta wannan

Batun jirgin Nigeria Air: Hadi Sirika ya tono asiri, ya ce dan majalisa ya nemi cin hanci

Lauyan ne ya binciki duka kudin da Akanta Janar ya biya jihar Delta tun daga 2007 zuwa 2022. Binciken ya nuna bin da aka biya Delta shi ne N1.76tr.

Ba a biya DESOPADEC kasonsu ba?

A cewar jagoran na PANDEF, a doka ya kamata gwamnan ya bada 50% na kason kudin ga DESOPADEC, amma Okowa ya rike komai a hannunsa.

Tsohon gwamnan ya karyata zargin da ya yi magana ta bakin Charles Aniagwu inda ya zargi Clark da taso shi gaba saboda sabanin siyasa a zaben 2023.

Tinubu ya saye Ben Murray Bruce?

Da canjin da aka yi a tsarin kudin kasashen waje, an ji labari Ben Murray Bruce ya ce Bola Tinubu ya kawo karshen masu kasuwanci da alfarmar gwamnati.

Tsohon Sanatan ya ce a baya ana ba shafaffu da mai iznin shigo da kaya daga kasashe waje a gwamnati Jigon PDP ya nuna hakan ya zo karshe a yau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng