Har Amnesty International Ta Fadi Adadin Mutanen da Aka Kashe a Gwamnatin Tinubu
- Amnesty International ta na cigaba da bin lissafin duk wasu kashe-kashe da miyagu su ka yi a Najeriya
- Kungiyar kare hakkin Bil Adamar ta ce alkalumanta sun nuna an kashe mutum 120 a zamanin Bola Tinubu
- Shugaban Amnesty International ya ce dole ne gwamnatin Bola Tinubu ta dage wajen kare jinin al’umma
Abuja - Kungiyar nan ta Amnesty International mai ikirarin kare hakkin Bil Adama, ta yi magana a game da kashe-kashen da ake yi a Najeriya.
A wani bayani da aka samu a shafin kungiyar, an ji cewa sabon Darektanta na Najeriya, Isa Sanusi ya ce an zubar da jini a ‘yan kwanakin nan.
Mista Sanusi wanda shi ne shugaban rikon kwarya na Amnesty International, ya ce mutum akalla 123 su ka mutu daga 29 ga watan Mayu zuwa yau.
A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne Bola Ahmed Tinubu ya karbi mulki a hannun Muhammadu Buhari, ya dare kan kujerar shugabancin Najeriya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jawabin shugaban Amnesty Int'l
“Abin tsoro ne cewa hare-haren ‘yan bindiga sun ci akalla mutane 123 makonni kadan da hawan Shugaba Bola Tinubu kan mulki a ranar 29 ga Mayu.
Kauyuka da kullum su ke zaune a shirin kawo hari, su na fuskantar munanan kashe-kashe. Dole gwamnatin nan ta maida hankali a kare rayuka.
Ya zama dole hukumomin Najeriya su dauki matakin gaggawa domin hana cigaba da zubar da jini.
Gazawar hukuma wajen kare mutanen Najeriya ya na neman zama ba-komai ba a kasar nan. Gwamnatin nan ta yi alkawarin ba jama’a kariya.
Sai dai har yanzu ba a cika alkawarin nan ba, ba a ga wani yunkurin kirki daga gwamnatin Najeriya wajen bada kariya ga al’umma masu rauni ba.
Yan Gidan Magajiya Sun Harzuka Sun Maka Kwastoma A Kotu Kan Tura Musu Alat Na Bogi Bayan Sun Gama Harka
- Isa Sanusi
Ya kamata ayi bincike na musamman
Sanusi ya bukaci a binciki duka kashe-kashen da aka yi domin a hukunta masu wannan danyen aiki.
Kungiyar ta ce an rasa rayuwa fiye da 150 kauyukan Mangu, Katako da Kusherki a jihar Filato, sannan an kashe Bayin Allah sama da 100 a Benuwai.
A jihar Kaduna, mutane fiye da 100 ‘yan bindiga su ka hallaka daga Disamba zuwa Afrilu.
Tinubu ya cika alkawarinsa
A wani rahoto da mu ka fitar, an ji labari matakin da Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya dauka zai yi sanadiyyar arzikin matasa da-dama a kasar nan.
Mutum kusan rabin miliyan daya ake hasashen sabuwar dokar kare bayanai za ta nemawa aiki. Tinubu ya fara cika alkawuran da ya yi wajen kamfe.
Asali: Legit.ng