Binciken Kwakwaf: Shugaban Kasa Bola Tinubu Bai Nada Ministoci 27 Ba
- Jerin sunayen sabbin nade-nade da wasu sabbin ma'aikatu da shugaban kasa Bola Tinubu ya samar na ta yawo a Facebook
- Sai dai kuma, rahoton wani binciken kwakwaf ya gano jerin sunayen na bogi ne, yana mai cewa babu wata sanarwa a hukumance daga fadar shugaban kasa
- Jerin sunayen ya yi ikirarin cewa an nada Femi Falana a matsayin ministan shari'a, Pat Utomi a matsayin minidtan ci gaba da tsare-tsaren kasa
An gano cewa jerin sunayen sabbin nade-nade 27 da wasu sabbin ma'aikatu da ake zargin shugaban kasa Bola Tinubu ya samar kuma suka karade Facebook na bogi ne.
Kamar yadda Africa Check, wani dandamalin binciken kwakwaf ya rahoto, ana ta yada jerin sunayen mutanen 27 wanda aka tabbatar da karya ne, a shafukan Facebook, tare da ikirarin cewa shugaban kasa Tinubu ya soke wasu kujerun ministoci.
A bisa ga wallafar ta Facebook, an nada shahararren faston Najeriya, Tunde Bakare a matsayin mai ba Tinubu shawara ta musamman yayin da aka nada Pat Utomi, masanin tattalin arziki kuma jigon jam'iyyar Labour Party a matsayin ministan ci gaba da tsare-tsaren kasa.
Rahoton ya kuma ce an nada mai rajin kare hakkin dan adam, Femi Falana a matsayin ministan shari'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ku yi watsi da sunayen, Utomi ga yan Najeriya
Daya daga cikin sunayen da ke jerin takardar, Utomi, ya karyata ikirarin cewa an nada shi mukamin minista a gwamnatin Tinubu. Utomi ya bukaci yan Najeriya da su yi watsi da sunayen, jaridar Punch ta rahoto.
Tsarin nada ministoci
Ku tuna cewa wani kudiri da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiwatar, ya yi umurnin cewa sabuwar gwamnari ta nada ministoci cikin kwanaki 60.
Sannan sai a aika sunayen don yan majalisa su tantance sunayen ministocin da aka aika a majalisar dokokin tarayya.
Akwai yiwuwar a watsa shirye-shiryen tabbatar da sunayen a majalisar dokoki kai tsaye kamar yadda aka saba yi a baya.
Babu wani abu mai kama da wannan da ya faru kuma babu kafar watsa labarai da ta kawo rahoton irin haka tun da shugaban kasa Tinubu ya hau karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya rage alawus din yan NYSC? Gaskiya ta bayyana
A wani labarin, mun ji cewa an gano cewa hotuna da dama da masu amfani da dandalin WhatApp suka daura a shafukansu na ikirarin cewa Shugaban kasa Bola Tinubu na shirin rage alawus din da ake ba yan bautar kasa (NYSC) ba gaskiya bane.
Dubawa ta rahoto cewa binciken kwakkwafi da aka yi kan rantsar da Tinubu ya nuna cewa bai taba yin wannan sanarwar a jawabinsa ba.
Asali: Legit.ng