Gwamnatin Tinubu Zata Fara Rabawa Daliban Bashi Daga Watan Satumba

Gwamnatin Tinubu Zata Fara Rabawa Daliban Bashi Daga Watan Satumba

  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ba da umarnin a fara bai wa ɗaliban Najeriya rance daga watan Satumba, 2023
  • Babban sakataren ma'aikatar ilimi, David Adejo, ya ce wannan tsarin zai taimaka wa kowane ɗan Najeriya ya samu ilimi mai nagarta
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan shugaɓa Tinubu ya rattaɓa hannu a kan kudirin bashin ɗalibai ranar Litinin

Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin jagoranci shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ta ce tana aiki ba dare ba rana domin ganin an fara bai wa ɗaliban Najeriya bashin kuɗi a watan Satumba da Oktoba, 2023.

Babban Sakataren ma'aikatar ilimi, David Adejo, ne ya sanar da haka ranar Laraba yayin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida a birnin tarayya Abuja.

Bola Ahmed Tinubu, shugaban Najeriya.
Gwamnatin Tinubu Zata Fara Rabawa Daliban Bashi Daga Watan Satumba Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Idan baku manta ba, shugaba Tinubu ya rattaɓa hannu kan kudirin bai wa ɗaliban Najeriya rancen da babu kuɗin ruwa ranar Litinin da ta gabata, kamar yadda The Cable ta tattaro.

Kara karanta wannan

Sanatan APC: Kar Wanda Ya Ga Laifina Idan Sabon Shugaban Majalisar Dattawa Ya Bai Wa Yan Najeriya Kunya

Menene alfanun wannan tsari ga yan Najeriya?

A jawabinsa, babban Sakataren ma'aikatar ilimi, Mista Adejo, ya ce wannan tsarin zai sauƙaƙa wa 'yan Najeriya su samu ilimi ciki sauƙi ta hanyar karɓan bashin da ba kuɗin ruwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka zalika, ya yi bayanin cewa shugaba ya rattaɓa hannu kan kudirin dokar ne domin tabbatar da kowane ɗan Najeriya ya samu ilimin manyan makarantu ta hanyar "Abinda muka raɗa wa, Bankin ilimi."

Vanguard ta rahoto Mista Adejo na cewa:

"Mun ɗauki darasi, wannan bankin ba zai tsaya iya karban takardun neman bashi ba, zai yi aiki yadda kowane baki ke aiki kuma ya tabbatar ana ba da bashin saboda a baya mun sha fama wajen dawo da kuɗin da aka ranta."
"A yau da nake magana da ku, shugaban kasa ya kafa kwamiti wanda ya ƙunshi ma'aikatu da hukumomi kuma zasu fara zama ranar 20 ga watan Yuni."

Kara karanta wannan

Cikakken Jerin Sunayen Shugabannin Majalisun Tarayya Na 10, Muƙamai, Da Jihohin Da Suka Fito

"Haka nan shugaban kasan ya ba da umarni cewa daga nan zuwa tsakanin Satumba da Oktoba na wannan zangon karatun 2023/2024, yana son ganin shaidar waɗanda suka ci gajiyar rancen."

Bisa haka ya ce daga nan zuwa wannan lokaci da shugaban kasa ya ba da umarni, ana fatan fara bai wa ɗalibai bashin mara kudin ruwa.

Majalisar Dokokin Kano Ta Amince da Bukatar Abba Gida-Gida Ya Nada Hadimai 20

A wani rahoton na daban Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi kira da Abba Gida-Gida ya aike da wasiƙar neman naɗa hadimai 20 ga majalisar dokokin jihar.

Kakakin majalisar dokokin jihar, Isma'il Falgore, ya karanta takardar mai girma gwamna a zaman mambobi na yau Laraba, 14 ga watan Yuni, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262