Yan Gidan Magajiya Sun Harzuka Sun Maka Kwastoma A Kotu Kan Tura Musu Alat Na Bogi Bayan Sun Gama Harka
- Wasu 'yan gidan magajiya sun gurfanar da matashi mai suna Oluwafemi Damilola a gaban kotun Magistare bisa zargin damfara
- Matan sun ce Damilola ya tura musu sakon banki na bogi bayan ya kwana da su a watan Oktoba na shekarar 2022 a birnin Ondo
- Mai shari'a, Mrs Charity Adeyanju ta umarci wanda ake zargin da ya biya kudin kafin dawowa ci gaba da sauraran karar a ranar 23 ga watan Yuni
Jihar Ondo - An gurfanar da wani matashi mai suna Oluwafemi Damilola a gaban kotun Magistare da ke jihar Ondo bisa zargin kin biyan wasu mata hakkinsu bayan ya kwana da su har N45,000.
Wanda ake zargin ya damfari mata guda huɗu masu suna Glory David da Akere Bright da Valria Isaac da kuma Ngozi Okoro yayin da ya tura musu sakon banki na karya.
Dan sanda mai gabatar da kara, Akao Moremi ya fadawa kotu cewar wanda ake zargin ya aikata laifin a watan Oktoba na shekarar 2022 a hanyar Sabo da ke birnin Ondo, cewar Leadership.
Matashin ya damfari 'yan gidan magajiya N45,000
Mai gabatar da karan ya ce zai iya kawo shaidu guda biyar don su tabbatar da faruwar hakan, yayin da ya bukaci kotun ta ba shi lokaci don yin nazari akai.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Lauyan wanda ake kara, Mrs S. A Iluyemi ya roki kotun da ta sake Damilola inda ta yi alkawarin cewa zai biya kudin kafin dawowa ci gaba da sauraran karar.
Mai shari'a Adeyanju ta umarci matashin ya biya kudin kafin dawowa kotun
Da take yanke hukunci, Mrs Charity Adeyanju ta amince da bukatar lauyan wanda ake karar inda ta umarce shi da ya biya kudin kafin dawowa ci gaba da sauraran karar, cewar rahotanni.
Ta kuma umarci masinjan kotun da ya tabbatar an biya kudin da kawo rahoto gaban kotun don tabbatarwa.
Ta dage ci gaba da sauraran karar har zuwa 23 ga watan Yuni.
Wani Ya Damfari Yar Gidan Magajiya A Abuja, Bai Biya Ta Kudin Aiki Ba
A wani labarin, wata kotu da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin tsare matashi mai suna Victor Emeka bisa zargin cutar 'yar gidan magajiya.
Dan sanda mai gabatar da kara ya ce ana zargin Victor da zamba cikin aminci wanda ya musanta.
Alkalin kotun, Saminu Sulaiman ya umarci a tsare wanda ake zargin zuwa ranar 5 ga watan Mayu don ci gaba da shari'ar.
Asali: Legit.ng