Tinubu Ya Yi Magana Kan Hadarin Kwale-Kwalen Da Ya Yi Sanadin Rasa Ran Mutane 103, Ya Bukaci A Yi Bincike

Tinubu Ya Yi Magana Kan Hadarin Kwale-Kwalen Da Ya Yi Sanadin Rasa Ran Mutane 103, Ya Bukaci A Yi Bincike

  • Shugaba Tinubu ya bayyana baƙin cikinsa kan hadarin kwale-kwale a jihar Kwara da ya yi sanadin mutuwar mutane aƙalla 100
  • Ya ba da umarnin gudanar da bincike kan musabbabin faruwar haɗarin, da kuma ba da umarnin bayar da agajin gaggawa ga waɗanda suka tsira da rayukansu da iyalan wadanda abin ya shafa
  • Tinubu ya yi alƙawarin magance ƙalubalen da ake fuskanta a sufurin ruwa a cikin ƙasar nan don tabbatar da tsaro da bin ƙa'idojin aiki

Abuja Shugaban ƙasa Bola Tinubu a ranar Laraba, ya bayyana baƙin cikinsa dangane da hadarin kwale-kwalen da ya afku a jihar Kwara, wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutane 100.

Shugaban ya kuma umurci hukumomin da abin ya shafa da su gano musabbabin faruwar hadarin, tare da kuma ba da agajin gaggawa ga waɗanda suka tsira da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

Kara karanta wannan

Gwara Haka: A Kokarin Tserewa Sojoji Mai Garkuwa Da Mutane Ya Sheka Barzahu

Shugaba Tinubu ya jajantawa waɗanda haɗarin kwale-kwale ya rutsa da su
Tinubu ya jajantawa waɗanda haɗarin kwale-kwale ya rutsa da su, ya buƙaci a yi bincike. Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Tinubu ya jajantawa waɗanda haɗarin kwale-kwale ya rutsa da su

Sakon ta’aziyyar Tinubu na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun daraktan yada labarai na fadar Gwamnatin Tarayya, Abiodun Oladunjoye, mai taken ‘Shugaba Tinubu ya jajanta wa wadanda hatsarin jirgin ruwan Kwara ya rutsa da su, ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike.’

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar The PUNCH ta ruwaito cewa hadarin kwale-kwalen ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 100 wadanda suka halarci ɗaurin aure a ƙauyen Egbu da ke ƙaramar hukumar Pategi a jihar.

A kalaman na Shugaba Tinubu:

"Na yi matukar bakin ciki da labarin hatsarin jirgin ruwa da ya yi sanadin mutuwar mutanenmu a jihar Kwara."
"Cewa waɗanda abin ya rutsa da su yan zuwa ɗaurin aure ne ya ƙara sanya hatsarin zama mai ƙuna a rai."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Tinubu Ya Rattaɓa Hannu Kan Kudirin Bai Wa Ɗaliban Najeriya Bashin Kuɗi

"Ina miƙa ta'aziyyata ga iyalai da abokanan waɗanda abin ya shafa."

Tinubu ya ba da umarnin a gudanar da bincike kan musabbabin haɗarin

Tinubu ya kuma jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Kwara kan mummunan hadarin. Sannan ya yi addu'ar Allah ya bai wa iyalan waɗanda suka rasu haƙurin jure rashin.

Shugaban ya kuma buƙaci gwamnatin jihar Kwara da hukumomin Gwamnatin Tarayya da abin ya shafa da su duba musabbabin haɗarin jirgin ruwan.

Sannan Tinubu ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta magance ƙalubalen da ake fuskanta a harkokin sufurin ruwa a cikin kasar nan don tabbatar da tsaron lafiya da bin ƙa'idojin aiki.

PM News ta ruwaito cewa, Tinubu ya ba da umarnin a raba kayan agaji ga waɗanda suka tsira da kuma iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

Abba Gida Gida ya yi bayani kan dalilin rushe shatale-talen gidan gwamnati

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa a baya, kun karanta cewa gwamnan jihar Kano, Abba Gida Gida ya bayyana dalilan da yasa ya bada umarnin rusa shatale-talen da ke a ƙofar gidan gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda Ya Kwace Filayen da Gwamnatin Masari Ta Raba Wa Mutane a Katsina, Ya Faɗi Dalili

Da safiyar yau Laraba ne dai aka tarar da cewa, gwamnati ta sa an rushe shatale-talen cikin daren da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng