Dattijon Arewa, Jigon NNPP Ya Yabi Tinubu, Ya Hango Alheri Ga 'Yan Najeriya

Dattijon Arewa, Jigon NNPP Ya Yabi Tinubu, Ya Hango Alheri Ga 'Yan Najeriya

  • Jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya bayyana cewa matakan da Shugaba Bola Tinubu ke dauka za su kawo sauyi a kasar
  • Galadima ya bayyana haka ne a ranar Litinin 12 ga watan Yuni yayin bikin bude gidan cin abinci na Nuite De-Paris na wata 'yar kasar Iran a Abuja
  • Ya ce Tinubu a matsayinsa na dan jam'iyyar APC ya dauko hanyar gyara kasar musamman irin matakan da yake dauka a kwanan nan

FCT, Abuja - Jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya ce matakan da Shugaba Bola Tinubu ya ke dauka za su kawo ci gaba a Najeriya.

Buba Galadima ya bayyana haka ne yayin taron bude gidan cin abinci na Nuite De-Paris a ranar Litinin 12 ga watan Yuni a Abuja.

Buba Galadima ya yabi Shugaba Tinubu
Jigon NNPP Ya Yango Alheri Ga 'Yan Najeriya. Hoto: The Whistler NG.
Asali: Facebook

Galadima ya ce Tinubu ya dauko hanyar gyara kasar nan

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawar Sirri Da Matasan Jam'iyyar APC Kan Batun Ministoci

Ya ce Tinubu a matsayinsa na dan jam'iyyar APC ya dauko hanyar gyara kasar inda ya bukaci shugaban da ya ci gaba da aikin da ya sa a gaba, cewar TheCable.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

"Mu da muka shafe shekaru 45 a harkar siyasa, kowa yasan a yanzu bambancin a bayyane yake.
"Muna yabawa shugaban kasa har yanzu bai bamu kunya ba saboda yana kan hanya.
"Muna addu'a da sa ran wannan mutumi mai jini a jiki zai ci gaba da wannan aiki don ciyar da kasar gaba."

Folasade Tinubu-Ojo 'ya ga shugaban kasa ta bayyana goyon bayanta ga matasa

Da take jawabi, 'yar shugaban kasa, Folasade Tinubu-Ojo ta ce tana goyon bayan 'yan kasuwa da ke kokarin samar da ayyukan yi ga matasa, cewar rahotanni.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Mataimakin Shugaban APC Na Ƙasa Da Ke Adawa Da Ganduje Ya Yi Murabus, Ya Fadi Dalili

A nata jawabin, Maria Namvar wacce ita ce mai gidan ci abincin, ta ce za ta ci gaba da kawo irin wadannan Najeriya saboda akwai abubuwan ci gaba a kasar.

Abin da Ya Hana Kwankwaso Zuwa Kotu Don Kalubalantar Zaben Shugaban Kasa, Buba Galadima

A wani labarin, jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya bayyana dalilin da ya hana Kwankwaso zuwa kotu kan zaben shugaban kasa.

Ya ce sun ki suje kotu ne saboda suna son kasar Najeriya ta ci gaba, zuwa kotun zai kawo wasu matsaloli na daban.

Dan siyasar ya ce ba su son lalata zaben da aka yi shiyasa suka hakura da zuwa kotun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.