Akwai Dalili: Abba Gida Gida Ya Fadi Hikimar Ruguza Shatale-Talen Gidan Gwamnati

Akwai Dalili: Abba Gida Gida Ya Fadi Hikimar Ruguza Shatale-Talen Gidan Gwamnati

  • Gwamnatin jihar Kano ta ruguza sanannen shatel-talen nan da yake kusa da kofar gidan Gwamnati
  • Zuwa yanzu ba a ji dalilin hakan ba, amma sabon Gwamna, Abba Kabir Yusuf ya dage da rushe-rushe
  • Daga baya Mai girma Gwamnan Kano ya fito ya yi bayanin da ya sa aka dauki wannan mataki

Kano - Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnatin jihar Kano ta ruguza shatale-talen da yake gaban kofar shiga gidan gwamnati.

A daren yau ne aka ji motar ruguza gini ta dura kan wannan shatale-tale, tayi ta rusa shi, har ta kai shi kasa, sai dai aka ga hotuna da safe.

Mutane sun wayi gari sun ga babu ginin kamar yadda tashar rediyon Freedom ta rahoto.

Abba da Rushe-Rushe
Hanyar shiga gidan Gwamnatin Kano Hoto: kanofocus.com
Asali: UGC

"Gara a rusa shi"

Wadanda su ke goyon bayan sabon Gwamna watau Abba Kabir Yusuf sun ce babu abin da shatale-talen yake jawowa illa cinkosoa yankin.

Kara karanta wannan

Rusau a Kano: APC Ta Maida Raddi Ga Gwamna Abba Gida-Gida, Ta Roke Shi Alfarma 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A gefe guda kuwa, Legit.ng Hausa ta fahimci jama’a da-dama su na ganin babu dalilin rusa ginin domin ba a saba wata ka'ida a ginin ba.

An komawa filin Idi

A gefe guda, gidan rediyon ya kawo rahoto cewa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta cigaba da rushe-rushe a Masallacin idin na kofar mata.

Arch. Ibrahim Yakubu wanda shi ne Shugaban hukumar tsara birane ta Kano ya ce hakan zai bada dama ayi sallar idi mai zuwa cikin dadi.

Yakubu ya gargadi mutane su dauke kayansu daga duk inda hukuma tayi wa jan fenti.

Matsayar doka – Barista Hikima

Legit.ng Hausa tayi magana da Abba Hikima wanda Lauya ne a garin Kano a game da abubuwan da ke faruwa na ruguje wasu wurare.

Barista Hikima ya ce tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ya rika amfani da doka ya mallakawa na kusa da shi filaye da dukiyar gwamnati.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Ci Gaba Da Aikin Rusau Bayan Zazzafan Musayar Yawu Da Aka Yi Tsakanin Ganduje Da Kwankwaso

Lauyan yake cewa duk da wadanda aka ba filayen sun mallaki takardun CofO, an saba tsarin gina birnin tun farko a wajen yanka filayen.

Amma duk da ya na goyon abin da yake faruwa, masanin shari’ar ya yi magana a shafin Facebook, ya soki rusa shatele-talen da aka yi.

Gwamnatin Kano ta fitar da jawabi

Jawabi ya fito daga Sanusi Dawakin Tofa, ya na cewa saboda sha’anin tsaro aka ruguza ginin, kuma gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta sake gina wani.

Sakataren yada labaran Gwamnan na jihar Kano ya ce an tuntubi kwararru, kuma sun shaida cewa shatale-talen zai iya rushe tsakanin shekarar 2023 da 2024.

D/Tofa ya ce tun farko ba ayi ginin da kankaren da ya dace ba, baya ga haka ya na kawo matsalar cinkoso a titi, kuma tsawonsa ya zama barazana ga tsaro.

Magana ta kai Aso Rock

A makon jiya aka ji labari Bola Tinubu ya gayyaci Rabiu Kwankwaso zuwa fadar Aso Villa a kan rushe-rushen da ake yi a garin Kano.

Kara karanta wannan

Dakatar Da Emefiele: "Tinubu Na Daukar Matakan Da Suka Dace a Kasar", Inji Tsohon Sanatan PDP

Kwankwaso ya fadawa shugaban kasa cewa tsohon Gwamna, Abdullahi Ganduje ya rika kwashe filayen talakawa, ya na ba iyalinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng