Abin da Ya Kai Ni Wajen Bola Tinubu – Jonathan a Kan Ziyararsa Zuwa Aso Rock

Abin da Ya Kai Ni Wajen Bola Tinubu – Jonathan a Kan Ziyararsa Zuwa Aso Rock

  • Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin Dr. Goodluck Ebele Jonathan wanda ya yi mulki kafinsa
  • Tsohon shugaban na Najeriya ya je fadar Shugaban kasa ne a kan ayyukan da yake yi a Afrika
  • Kungiyar ECOWAS ta zabi Jonathan ya sasanta rikicin kasar Mali, don haka ya yi zama da Tinubu

Abuja - A ranar Talata, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zauna da daya daga cikin magabantasa da suka mulki Najeriya, Mai girma Goodluck Jonathan.

Rahoto ya zo daga Channels cewa tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya zauna da Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa na Aso Rock.

A wannan zama wanda shi ne na farko tsakaninsu, Jonathan ya yi wa Bola Tinubu bayanin halin da ake ciki a kasar Mali da sauran kasahen Nahiyar.

Tinubu da Goodluck Jonathan
Bola Tinubu da Goodluck Jonathan a Aso Rock Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

A matsayin shugaban kwamitin sasanci da ECOWAS ta kasashen yammacin Afrika ta tura zuwa Mali, Jonathan ya yi bayanin yadda aka kwana.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Fastoci Sun Waigo Ga Tinubu da Wasu Bukatu, Sun Ce Dole ya Cika Musu Alkawari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

The Cable ta ce tsohon shugaban na Najeriya ya shaidawa manema labarai cewa ya sa labule da Bola Tinubu ne domin sanar da shin abin da ke faruwa.

“Na zo ne in yi wa shugaban kasa bayani a game da sha’anin wasu kasashe da nahiyar.
Ni ne mai sulhun ECOWAS a kasar Mali kuma ni ne shugaban kungiyar dattawan kasashen Afrika ta yamma.
Saboda haka akwai abubuwan da ke faruwa a iyakokin nahiyar da kasashe da kan jawo in zauna da shugabannin kasashe.

- Dr. Goodluck Jonathan

Lokacin da Jonathan ya iso Aso Rock

Shirin zaben kasar Mali

A ranar 19 ga watan Yunin nan ne kasar Afrika ta yamman za ta fito da sabon kundin tsarin mulki da za a rika amfani da shi a karkashn mulkin farar hula.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fadi Yadda Zai Rage Radadin Tashin Fetur, Ya Yabi Abiola da 'Yar'adua

An samu korafi daga musamman Musulman kasar wadanda su ne da rinjaye, su na zargin ana neman a raba Mali da harkar addini a sabon tsarin mulkin.

The Cable ta ce wannan ya na cikin batutuwan da Jonathan ya kai gaban sabon shugaban Najeriya yayin da mutanen Mali su ke shiryawa zabe a 2024.

"Tinubu ya taimakawa Akpabio" - Ndume

An rahoto Muhammad Ali Ndume ya na cewa Shugaban kasa ya lallaba ya ziyarci wasu ‘yan majalisa kuma ya roke su da su zabi Sanata Godswill Akpabio.

Sanatan ya ce Bola Tinubu ya goyi bayan Akpabio ne ganin ‘Yan kudu maso kudu ba su taba rike mukamin shugaban majalisar dattawa ba tun 1999 har yau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng