'Yan Daba Sun Sari Dalibin Jami'a a Jihar Bauchi Kan Gardamar Kwallon Kafa
- Wasu da ake zargin ƴan daba ne sun sari wani ɗalibin jami'a a jihar Bauchi bayan gardamar ƙwallon ƙafa ta ɓarke a tsakaninsu
- Ɗaya daga cikin ƴan daban ne dai ya sari ɗalibin mai suna Safiyanu Adamu da wuƙaƙe har guda biyu a hannunsa
- Ɗalibin yana can kwance a asibiti ana duba lafiyarsa biyo bayan wannan aika-aika da aka tafka masa a kan ƙwallon ƙafa
Jihar Bauchi - Ƴan daba sun sari wani ɗalibi mai suna Safiyanu Adamu, na jami'ar Sa'adu Zungur, da ke a Gadau a jihar Bauchi bayan ɓarkewar gardamar ƙwallon ƙafa.
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa, lamarin ya auku ne lokacin da ake wasan ƙwallo a tsakanin Green-White-Green House da GT House a ranar Asabar, inda ɗaya daga cikin ƴan daban ya caka masa wuƙa.
Ranar Dimokuradiyya: Dalilai 5 Da Suka Sa Ranar 12 Ga Watan Yuni Ke Da Muhimmanci A Tarihin Najeriya
Ɗan daban dai ya cakawa ɗalibin wuƙa ne a wuyan hannunsa na dama bayan gardamar ta rikiɗe ta koma faɗa.
Ɗaliɓin yana kwance a asibiti
Safiyanu Adamu wanda yanzu haka ake duba lafiyarsa a babban asibitin tarayya da ke Azare, ya bayyana cewa ana cikin wasan wani da ake kira Lado yaje gida ya ɗauko wuƙaƙe biyu waɗanda ya sare shi da su a hannunsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun nuna cewa ɗaliban da suka yi ta maza suka tsaya da sauran wasu mutane sun ceto shi inda suka garzaya da shi babban asibitin Gadau, domin duba lafiyarsa.
An ba Safiyanu kulawar farko a babban asibitin na Gadau kafin daga bisani aka wuce da shi zuwa babban asibitin tarayya na Azare domin ba shi cikakkiyar kulawa.
Lokacin da aka nemi jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Ahmed Wakili, ya bayyana cewa zai tuntuɓi DPO ɗin yankin kan lamarin kafin ya bayyanawa ƴan jarida halin da ake ciki.
Sai dai, wani ɗan sanda a Gadau ya bayyanawa ƴan jarida cewa suna bakin ƙoƙarinsu wajen yayyafawa lamarin ruwan sanyi kada ya rikiɗe zuwa rikici bayan ɗaliban sun fara shirin ɗaukar fansa.
Ya ce ƙoƙarin na ƴan sanda ya haifar da ɗa mai ido domin zaman lafiya ya dawo a garin inda kowa ya ci gaba da gudanar da harkokinsa.
Yan Daba Sun Lakada Wa Dan Takarar Gwamnan PDP Duka
A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa ɗan takarar gwamnan jam'iyyar PDP a jihar Ogun, ya sha da kyar a hannun ƴan bindiga bayan sun laƙada masa dukan tsiya.
Segun Showunmi tsautsayi ya faɗa masa ne bayan yaje kotu sauraron zaman shari'ar ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar.
Asali: Legit.ng