Gwamnan Ondo Ya Dauki Hutun Rashin Lafiya, Ya Mika Mulki Ga Mataimakinsa

Gwamnan Ondo Ya Dauki Hutun Rashin Lafiya, Ya Mika Mulki Ga Mataimakinsa

  • Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya ɗauki hutun kwanaki 21 domin zuwa neman lafiya a ƙasar waje
  • Wannan na ƙunshe ne a wata wasiƙa da mai girma gwamnan ya aike wa majalisar dokokin jihar ranar Talata 13 ga watan Yuni, 2023
  • Akeredolu ya sanar da majalisar cewa zai miƙa baki ɗaya harkokin mulki ga mataimakinsa gabannin ya dawo ranar 6 ga watan Yuli

Ondo - Majalisar dokokin jihar Ondo ta tabbatar da cewa ta karɓi wasiƙar neman hutun tafiya duba lafiya daga gwamnan jihar, Arakunrin Oluwarotimi Odunayo Akeredolu.

A rahoton TVC News, kakakin majalisar dokokin jihar Ondo, Olamide Oladiji, ne ya sanar da batun tafiyar gwamnan zuwa ganin likita a ƙasar waje.

Gwamna Akeredolu na jihar Ondo.
Gwamnan Ondo Ya Dauki Hutun Rashin Lafiya, Ya Mika Mulki Ga Mataimakinsa Hoto: Rotimi Akeredolu
Asali: Facebook

Da yake jawabi a madadin mambibin majalisar, kakakin majalisar, Olamide Oladaji, ya ce gwamna Akeredolu ya ɗauki hutun kwanaki 21 domin zuwa ganin likita saboda rashin lafiyar da yake fama da ita.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da Ya Kamata ku sani Game da Akpabio, Sabon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya

Kakakin majalisa ya ƙara da bayanin cewa hutun gwamnan ya fara ne daga ranar 7 ga watan Yuni, 2023 zuwa ranar 6 ga watan Yuli, 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar wasiƙar mai girma gwamna, hutun kwana 21 da ya ɗauka, wanda ya fara daga ranar 7 ga watan Yuni, an tsawaita shi zuwa 6 ga Yuli saboda ranakun hutun da suka faɗo a ciki.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa ranakun hutun da suka shiga cikin wannan lokaci sun haɗa da Hutun ranar Demokuraɗiyya, 12 ga watan Yuni da kuma hutun babbar sallah, 28 da 29 ga watan Yuni, 2023.

Gwamnan ya miƙa mulki ga mataimakinsa

Haka zalika wasiƙar ta yi bayanin cewa dukkan harkokin mulki sun koma hannun mataimakin gwamna, Lucky Orimisan Aiyedatiwa, wanda zai yi aiki a matsayin muƙaddashi har zuwa dawowar gwamna.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Tinubu, Gwamnan APC Ya Faɗi Sanatan da Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa

Bugu da ƙari, gwamna Akeredolu, ya tabbatar wa majalisar dokoki da ɗaukacin al'ummar jihar Ondo cewa zai koma baki aiki ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli, 2023, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Shugaban Majalisar Dattawa, Akpabio, Ya Ziyarci Shugaba Tinubu a Villa

A wani labarin na daban kun ji cewa sabon shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya shiga ganawa da shugaba Tinubu a Aso Rock.

Sauran waɗanda suka shiga wannan taro sun haɗa da gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262