Matashiya Ta Baiwa Direba N10K Saboda Ya Caje Ta N2500 Duk Da Zirga-Zirgar Da Ya Yi Da Ita
- Wata mata ta dauki tashar motar wani direba mai fara'a wanda ke fama da matsin rayuwa
- Ta biya shi N10,000 maimakon N2500 ya caje ta kuma hakan ya sa shi zub da hawaye tare da yi mata godiya
- Matar direban ta kirata washegari sannan ta yi mata godiya a kan karamcin da ta nuna masu
Wata mata da ke zaune a Port Harcourt ta wallafa labari mai taba zuciya na haduwarta da wani direba wanda ke cikin mawuyacin hali.
Matar mai suna Chukwudi Mmesoma a Facebook, ta dauki tashar mota daga gareji zuwa inda za ta a cikin wata farar mota Rav 4 fara sabuwa.
Ya kunna na'urar sanyaya wuri
Direban, wanda ya kasance magidanci a ganiyar shekaru 50 da yan doriya, ya kasance mutum mai kankan da kai da kuma faraha.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya bar na'urar sanyaya wuri a kunne duk da tsadar farashin man fetur harma ya fada mata inda za ta iya samun abinci ta siya.
Direban ya jira Mmesoma na kimanin mintuna 30 yayin da ta siya abincinta a wajen siyar da abinci na Genesis.
Ta lura cewa direban na yawan yin ihu a yan tsakanin tukin da yake yi, kamar dai yana tuna wani abun bakin ciki, sannan sai ya gaggauta bayar da hakuri.
Halin da yake ciki ya taba ta
Mmesoma ta ji tausayin mutumin amma bata son neman bin diddigi kan abun da ke damunsa wanda yake sirrinsa ne.
Da suka isa inda za ta sauka, direbay ya duba farashin sai ya ga N2500 ne.
Sai matar ta yanke shawarar yi masa alkhairi inda ta aike masa N10,000 maimakon kudin da ya kamata ta biya.
Direban ya kadu sannan ya cika da mamakin wannan karamci nata wanda ya sanya shi zubar da hawaye.
Washegari matar ta amsa kiran waya daga matar direban. Ta yi mata godiya sosai kan karamcin da ta nuna masu.
Matar ta yi godiya
Ta fada mata cewa mijinta ya dawo gida sannan ya sanar da ita komai. Ta bayyana cewa suna fama da matsalar rashin kudi da damuwa saboda hauhawan farashin man fetur da sauransu.
Ta ce karin kudin da ta yi masa ya taimaka masu sosai kuma ya kawo masu sauyi.
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin Jama'a a kasa:
Maryann Obiageli Azubuike ta yi martani:
"Yana da matukar kyau duk lokacin da ka taimakawa mutum mai kirki."
Dike Julia ta ce:
"Zan yi wa wani alkhairi yau da kullun."
Chinyere Paul ta rubuta:
"Mutane na matukar shan wahala. Allah ya kawo sauki. Nagode da kirkinki."
"Ina sonsa sosai": Matar aure ta saki hotunan sauyawar mijinta mai lalaurar shan inna
A wani labari na daban, wani bidiyo da ya yadu a TikTok ya nuna sauyawar wani matashi wanda ke da lalura ta shan inna.
Matar mutumin mai suna Jemimah wacce ta ce kyakkyawan mutumin mijinta ita ce ta wallafa bidiyon a kan manhajar TikTok.
Asali: Legit.ng