Bala'i Ya Auku Yayin Da Yan APC Suka Mutu A Hadarin Mota A Hanyar Zuwa Abuja
- Wasu mambobin jam'iyyar APC da ke tafiya zuwa Abuja daga Jihar Imo sun mutu a wani hadarin mota da ya afku ranar Litinin
- Rahotanni daga majiya da dama sun bayyana cewa, hadarin ya faru bayan karo da wata motar bas a Agbor da ke Jihar Delta
- Majiyoyin sun tabbatar da rasuwar mutane uku yayin da wasu da yawa suka jikkata kuma suke karbar magani a asibiti
Agbo, Delta - Wani abin bakin ciki ya faru kan wasu mambobin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, daga jihar Imo a ranar Litinin, 12 ga watan Yuni, a hanyarsu ta zuwa Abuja domin halartar kaddamar da yan Majalisar Tarayya da aka shirya a ranar Talata 13 ga watan Yuni.
Mambobin jam'iyyar na APC da magoya bayan jam'iyyar sun rasu a hadarin motar da ta yi karo da wata bas din a Agbor, Jihar Delta, The Punch ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jerin yan APC da suka rasu a hadari yayin da suke kan hanyar zuwa Abuja don halartar bikin kaddamar da majalisa ta 10
Rahotanni daga majiyoyi da dama sun bayyana cewa akalla mutum uku ne suka mutu yayin da dama ke asibiti suna karbar maganin raunuka daban daban da suka yi.
Daga cikin wanda suka rasu akwai mace daga yankin Ogbor da wasu maza biyu daga yankin Amaraku, yankunan na karkashin karamar hukumar Isiala Mbano da ke jihar.
Da yake bada labari bayan da ya nemi a boye sunansa, wani jigon jam'iyyar ya ce wanda abin ya shafa, magoya bayan zababben sanatan Imo ta Arewa ne, Patrick Ndubueze, da dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Okigwe ta Arewa, Mirriam Onuoha.
Yaushe za a kaddamar da majalisa ta 10?
Za a kaddamar da majalisa ta 10 ranar Talata, 13 ga watan Yuni, kuma ana sa ran yan majalisun biyu zasu zabi shugabannin majalisun biyu a ranar.
Kafin yanzu, jam'iyyar APC ta bayyana Godswill Akpabio, tsohon minista, a matsayin wanda ta sahalewa takarar kujerar shugabancin majalisar dattawa yayin da ta amince da Tajudeen Abbas a matsayin shugaban majalisar wakilai a majalisa ta 10.
Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Ba Wa Dalibai Rance
A wani rahoton Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin ba wa daliban Najeriya bashin kudi na zama doka.
Dele Alake, wakilin gwamnatin tarayya ne ya sanar wa manema labarai hakan a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Litinin.
Asali: Legit.ng