Yan Bindiga Sun Sace Sarakuna 2 Da Wasu Mutane a Jihar Bauchi

Yan Bindiga Sun Sace Sarakuna 2 Da Wasu Mutane a Jihar Bauchi

  • Yan bindiga sun kai hari kauyuka biyu a yankin karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Rahoto ya ce maharan sun kashe mutum ɗaya kana suka sace wasu mutum huɗu, ciki harda Dagattaj kauyukan
  • Hukumar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ce ba ta da tabbacin ko wanda aka harba ya mutu

Bauchi - Wasu mahara da ake tsammanin 'yan bindigan jeji ne sun halaka mutum ɗaya kana suka yi awon gaba da wasu mutane huɗu a yankin ƙaramar hukumar Ningi ta jihar Bauchi.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa daga cikin waɗanda maharan suka yi garkuwa da su a harin harda Sarakunan ƙauyukan Balma Anguwan Bakutunbe.

Harin yan bindiga.
Yan Bindiga Sun Sace Sarakuna 2 Da Wasu Mutane a Jihar Bauchi Hoto: leadership
Asali: Twitter

Wasu mazauna da lamarin ya faru a kan idonsu sun shaida cewa yan bindigan sun kai hari kauyukan biyu a lokuta daban-daban tsakanin daren Asabar da safiyar ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Ranar Dimokuradiyya: Dalilai 5 Da Suka Sa Ranar 12 Ga Watan Yuni Ke Da Muhimmanci A Tarihin Najeriya

Yadda yan bindiga suka kai hari kauyen Balma

Wani mazaunin Balma, wanda ya nemi a sakaya bayanansa, ya ce 'yan bindigan ɗauke da muggan makamai sun kai hari garin, suka buɗe wuta da misalin karfe 11:00 na safiyar Lahadi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce maharan sun wuce kai tsaye zuwa gidan Magajin Gari kuma suka yi awon gaba da shi bayan tsorata mutane da harbe-harben bindiga.

A cewarsa, yan bindiga sun kuma yi ajalin mutum ɗaya mai suna, Alhaji Haruna Dan OC, wanda kwararren likita ya tabbatar rai ya yi halinsa bayan an kai shi babban Asibitin Ningi.

Yadda maharan suka shiga Anguwan Bakutunbe

Haka nan kuma mahara sun shiga Bakutunbe, inda suka sace Magajin Gari, Idris Mai Unguwa, tare da wani mutum ɗaya mai suna, Ya’u Gandu Maliya.

Bayanai sun nun masu garkuwan sun nemi naira miliyan N8m kan kowane mutum ɗaya da suka sace a matsayin kuɗin fansa, kamar yadda rahoton Punch ya tabbatar.

Kara karanta wannan

“Guba Wani Ya Saka Musu A Abinci” An Tsinci Gawar Mata Da Miji Kwance Cikin Gidansu A Abuja

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar 'yan sanda reshen jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce:

"Hukumar yan sanda ta samu rahoto daga Balma, karamar hukumar Ningi cewa wasu 'yan bindiga sun kai farmaki, suka buɗe wa mutane wuta kana suka sace Mai gari, Alhaji Hussaini Saleh."
"Sun kuma harbi wani Jibrin a kai, nan take aka tura dakarun 'yan sanda suka ɗauki mutumin zuwa Asibitin Ningi domin a masa magani. Na fahimci an fara yaɗa cewa ya mutu, zan tutunɓeku bayan na yi magana da DPO."

Dakarun Soji Sun Halaka Yan Ta'adda, Sun Kwato Makamai a Jihar Kaduna

A wani labarin kuma Jami'an soji sun kai samame maɓoyar 'yan bindiga a Kaduna, sun samu nasarar sheƙe 'yan ta'adda.

Daraktan yaɗa labarai, Manjo Janar Musa Danmadami, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rattaɓawa hannu, ya ce sojin sun lalata sansanin 'yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Sauye-Sauye 5 Na Tinubu A Makonsa Na Biyu A Matsayin Shugaban Kasa Da Suka Girgiza Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel