An Kuma: Tsagera Sun Sake Yin Garkuwa Da Mai Sarautar Gargajiya A Arewacin Najeriya
- Gwamnatin jihar Plateau ta tabbatar da sace mai sarautar gargajiya a yankin Mushere da ke karamar hukumar Bokkos
- Gwamnan jihar, Caleb Mutfwang ne ya bayyana haka yayin da yake bayani a bikin ranar Dimokradiyya a ranar Litinin 12 ga watan Yuni
- Joshua Mutkut wanda shi ne Dagacin kauyen Mushere, maharan sun sace shi ne a ranar Lahadi da dare a fadarsa da ke kauyen
Jihar Plateau - Gwamnatin jihar Plateau ta tabbatar da sace mai sarautar gargajiya, Joshua Mutkut na kauyen Mushere da 'yan bindiga suka yi.
Joshua Mutkut shi ne Dagacin kauyen Mushere da ke karamar hukumar Bokkos ta jihar Plateau.
Jaridar Punch ta tattaro cewa maharan sun sace mai sarautar gargajiyan ne a ranar Lahadi 11 ga watan Yuni da dare a fadarsa da ke kauyen.
Gwamnan jihar Plateau shi ya tabbatar da faruwar lamarin yayin bikin ranar Dimukradiyya
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang shi ya bayyana hakan a ranar Litinin 12 ga watan Yuni yayin bikin ranar Dimokradiyya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Arewacin Najeriya na fama da hare-haren 'yan bindiga musamman a Arewa maso Yamma da kuma wasu jihohi a Arewa ta Tsakiya, cewar gidan talabijin na AIT.
Kakakin kungiyar matasa a yankin ya tabbatar da harin 'yan bindigan a Mushere
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin Kungiyar Matasa ta Yankin Mushere, Gashion Nahum ya ce maharan sun zo da yawa tare da rufe fuskokinsu a yayin harin yadda ba za a gane su ba.
Rundunar 'yan sandan jihar ta bakin kakakinta, DSP Alfred Alabo ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce yanzu haka jami'anta sun bazama neman maharan.
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a baya ya sha alwashin kawo karshen hare-haren 'yan bindiga musamman a wasu jihohi da ke Arewacin Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu ya karbi rantsuwar kama mulki daga tsohon shugaban kasa, Buhari a ranar Litinin 29 ga watan Yuni, 'yan kasar na ta hankoron ganin sauyi musamman ta fannin matsalar tsaro da ta addabi kasar.
Yadda Muka Rasa ’Yan Uwanmu a Harin ’Yan Bindiga, Mutane Sun Koka a Jihar Plateau
A wani labarin, 'Yan uwan wadanda hare-haren 'yan bindiga ya rutsa da su a jihar Plateau sun bayyana irin halin da suka shiga.
Harin wanda ya afku a ranar Talata 16 ga watan Mayu a karamart hukumar Mangu ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama.
Asali: Legit.ng