Tinubu Ya Fadi Yadda Zai Rage Radadin Tashin Fetur, Ya Yabi Abiola da 'Yar'adua

Tinubu Ya Fadi Yadda Zai Rage Radadin Tashin Fetur, Ya Yabi Abiola da 'Yar'adua

  • Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabi inda ya yi maganar wahalar da ake ciki bayan janye tallafin fetur
  • Sabon Shugaban kasar ya nuna cewa zai karkata wajen inganta jin dadi da rayuwar ‘Yan Najeriya
  • Mai girma Tinubu ya na ganin Mashood Abiola ya yi shahadar siyasar ne a yayin kare damukaradiyya

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya jinjinawa a kan Marigayi MKO Abiola wanda ake kyautata zaton ya na kan hanyar lashe zaben shugaban kasa a 1993.

Punch ta rahoto Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na bayyana Mashood Kashimawo Abiola wanda ya mutu a gidan yari a matsayin ayar damukaradiyya.

Da yake magana, Shugaban kasan ya yarda mutanen Najeriya su na shan wahala a sakamakon tashin da farashin man fetur ya yi saboda janye tallafi.

Bola Tinubu
Zaman Bola Tinubu da Sarakuna Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Alwashin da Tinubu ya sha

Kara karanta wannan

Wasa farin girki: Yadda tun farko Tinubu ya hango Emefiele na masa tuggu a zaben 2023

Bola Tinubu yake cewa gwamnatinsa za tayi wa al’umma sakayya ta hanyar gagaruman ayyukan more rayuwa a bangarorin sufuri da ilmin zamani.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban ya ce gwamnatin tarayya za ta maida hankali wajen samar da isasshen wutar lantarki, kiwon lafiya da sauran abubuwa na jin dadin rayuwa.

Tinubu yake cewa ya fahimci wahalar da ake sha, amma ya ce ba za a dawwama a wannan hali ba, ya kara da cewa janye tallafin fetur din ya zama dole.

MKO Abiola da zaben 93

Daily Trust ta ce ce Shugaba Tinubu ya jinjinawa Maraigayi MKO Abiola wanda ya kira shahidi a siyasa da ya mutu domin wanzurwar damukaradiyya.

"Na fahimci wahalar da ku ke sha. Matakin ya zama dole domin a ceci kasar mu, mu karbe dukiyoyin Najeriya a hannun wasu tsirarrun marasa kishi."

Kara karanta wannan

Da Dumi Dumi: Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Gwamnan CBN, Emefiele

Za mu iya tunawa da sadaukar da kai da shahadar Cif MKO Abiola, wanda ya yi nasara a zabe, amma sai aka soke zaben saboda mugun zalunci.
Ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare ginsikan damukaradiyya yadda mazaje da matan kasarsa su ka zabe shi a matsayin shugaban kasarsu."

- Bola Tinubu

Shugaban ya kuma yabi mutane irinsu Kudirat Abiola, Alfred Rewane da Manjo Janar Shehu Yar’Adua wanda ya ce sun mutu a kan tafarkin nan.

Shugaba Tinubu da 'Yan G5

A makon jiya rahoto ya zo Bola Tinubu ya yi zama da jiga-jigan PDP, Seyi Makinde, Nyesom Wike, Samuel Ortom, Okezie Ikpeazu da Ifeanyi Ugwuanyi.

Makinde ya fadi irin wainar da aka toya a lokacin da suka labule da sabon shugaban kasar. Wasu su na ganin sintirin Nyeson Wike ya fara yawa a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng