Betara da Gagdi Ya Janye Daga Takarar Shugabancin Majalisa, Sun Bar Wa Abbas Tajudden da Ben Kalu

Betara da Gagdi Ya Janye Daga Takarar Shugabancin Majalisa, Sun Bar Wa Abbas Tajudden da Ben Kalu

  • Alamu masu karfi na nuna yadda aka shawo kan Aliyu Betara wajen lallabarsa ya janye daga takarar shugabancin majalisa
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kwanaki ke kara matsowa na rantsar da majalisa ta 10 nan ba da jimawa ba
  • A tun farko, ‘yan siyasa da dama sun bayyana burin zama shugabannin majalisa a Najeriya, amma APC ta taka musu burki

FCT, Abuja - Ga dukkan alamu hanya na kara bullewa Tajuddeen Abbas da Benjamin Kalu a kokarinsu na zama kakakin majalisa da da mataimaki yayin da biyu daga cikin ‘yan takarar da ke kan gaba suka amince su janye tare da marawa matsayar APC baya.

Aliyu Betara daga jihar Borno da Yusuf Gadgi daga jihar Filato sun janye aniyarsu bayan wata ganawar sirri da suka yi da shugaba Bola Tinubu a gidansa, TVC News ta ruwaito

Kara karanta wannan

Ni ba barawo bane: Sanatan APC ya sharbi kuka a majalisa, ya fadi sharrin da aka masa

Ganawar ta samu halartar mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da kuma kakakin majalisar wakilai ta kasa Femi Gbajabiamila da gwamnan jihar Neja Mohammed Bago.

Betara ya janye daga takarar shugabancin majalisar wakilai
Yadda zaman majalisar kasa ke kasancewa | Hoto: channelstv.com
Asali: Facebook

Abin da aka tsayar a karshen ganawar

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya shaidawa manema labarai a karshen ganawar cewa, shugaba Tinubu ya ji dadin yadda Aliyu Betara da Yusuf Gagdi suka fifita muradun jam’iyyar APC sama da burinsu na kashin kai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma yi kira ga sauran masu neman kujerar da su yi koyi da mutanen biyu da suka yi watsi da burinsu tare da hada kai da jam’iyyar wajen samar da hadin kan kasa, daidaito da adalci, Vanguard ta tattaro.

A tun farko, jiga-jigan siyasa da dama ne suka bayyana fitowa neman kujerar kakakin majalisar, inda suka bayyana tasirinsu na siyasa da gudunmawar da suka bayar a matsayin hujja.

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisar Dattawa: Rahoto Ya Nuna Yan Majalisa Na Iya Siyar Da Kuri’unsu $5,000, $10,000 Ko Fiye da Haka

Sai dai, jam’iyyar APC ta bayyana cewa, ta zabi Tajuddeen Abbas a wannan aikin, don haka ta nemi goyon bayan sauran ‘yan majalisa.

Tinubu ya sa labule da manyan siyasa game da shugabancin majalisa

A wani labarin, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya sanya labule da wasu daga cikin ‘yan majalisar da ke neman kujerar kakakin majalisar wakilai ta 10, rahoton Tribune ya tabbatar.

Daga cikin ‘yan majalisar da shugaban ƙasan ya sanya labule da su sun hada da, Yusuf Gadgi, mai wakiltar Pankshin/Kanke a jihar Plateau, Sada Soli, mai wakiltar Jibia/Kaita a jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.