Yadda Tun Farko Tinubu Ya Hango Take-Taken Emefiele Ba Zai Haifar da da Mai Ido Ba
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya taba bayyana matsalar da ke tattare da manufar sauya fasalin Naira na babban bankin CBN karkashin Godwin Emefiele
- A yayin gangamin kamfen dinsa a filin wasa na MKO Abiola da ke Abeokuta, jihar Ogun, Tinubu ya ce manufar sauya fasalin Naira ba komai bane don kitsa masa sharri
- Tinubu, wanda daga baya ya ci zabe, ya yi rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga watan Mayu, ya kuma sanar da dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan CBN bayan haka
Abeokuta, Ogun – Kafin ya zama shugaban kasa, dan takarar shugaba kasa Bola Tinubu na jam’iyyar APC a wancan lokacin, ya yi tsokaci kan cewa manufar sauya fasalin Naira da babban bankin Najeriya (CBN) ya kawo ba komai bane sai shirin kawo masa cikas a zaben shugaban kasa na 2023.
Daga nan sai Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su bari sauyin ya raunana zukatansu wajen fitowa a lokacin zabe domin gudanar da aikinsu na ‘yancin ‘yan kasa don kada kuri’unsu.
Karancin Naira ba komai bane sai kokarin dakushe burina, Tinubu ya koka
Daga nan sai shugaban kasar mai ci a yanzu ya jaddada cewa karancin Naira da ake fama da shi a kasar nan zagon kasa ne ake masa kan ya fadi a zabe.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya kuma bayyana cewa, da gangan Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin CBN ya shirya hakan don haifar da rashin jituwa a tsakanin ‘yan Najeriya da jam’iyyar APC.
Tinubu ya yi wannan tsokaci ne a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun a yayin gangamin kamfen dinsa da ya gudana a babban filin wasa na MKO Abiola.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a wancan lokacin ya yi magana ne tare da karfafa gwiwa ga masu son kada kuri’unsu a zaben da ya gabata.
Tinubu ya bayyana cewa yana zuwa da “babban sauyi” a zaben 2023
Daga nan sai Tinubu ya bayyana cewa yana zuwa ne da “babban sauyi” wanda ya tsara shi domin juya al’amura su yi kyau a Najeriya tare da canza wa al’ummarta wahalhalu tare da daukaka darajar rayuwar talaka.
Daga nan sai ya lashe lashe zaben da aka yi a ranar Asabar 25 ga watan Faburairu, kana aka sanar a ranar 1 ga watan Maris.
Kimanin makwanni biyu da kama aikinsa na shugaban kasa, Tinubu ya sanar da dakatar da Emefiele a matsayin gwamnan CBN tare da ba da umarnin a bincike shi nan take.
Asali: Legit.ng