'Yan Sanda Sun Cafke Bata-Gari Mai Ba 'Yan Bindiga Da Safarar Makamai a Abuja

'Yan Sanda Sun Cafke Bata-Gari Mai Ba 'Yan Bindiga Da Safarar Makamai a Abuja

  • Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta yi babban kamun wani ƙasurgumim ɓata-gari mai haɗa baki da ƴan bindiga
  • Rundunar tace ta cafke ɓata-garin wanda ya gwanance wajen bayar da bayanai, safarar makamai da kayan abinci ga ƴan bindiga
  • Ƴan sanda sum kuma ƙwato makamai harsasai a hannun ɓata garin wanda rundunar ta dade tana nema ruwa a ajallo

Abuja - Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja, ta bayyana cewa ta cafke wani mai bayar da bayanai da safarar miyagun makamai da sauran kayayyaki ga ƴan bindigan da suka addabi birnin tarayya Abuja da kewayensa.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa kakakin rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ita ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa a birnin tarayya Abuja, a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-ɗumi: Wani Abu Ya Fashe, Ya Kama da Wuta a Yankin Birnin Tarayya Abuja

Yan sanda sun cafke mai ba ƴan bindiga bayanai a Abuja
Kakakin rundunar 'yan sandan birnin tarayya Abuja Hoto: @Jossy_Dannyking
Asali: Twitter

Adeh ta bayyana cewa jami'an ɓangaren rundunar mai yaƙi da garkuwa da mutane, su ne suka yi caraf da wanda ake zargin wanda aka daɗe ana nema ruwa a ajallo a dajin Mongoro.

Kakakin ta kuma bayyana cewa wanda ake zargin an cafke shi ne bisa hannun da yake da shi a wajen safarar miyagun makamai da suka haɗa da bindigu, harsasai da sauran makamai masu hatsari.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ƙware wajen safarar makamai ga ƴan binɗiga

Ta kuma bayyana cewa wanda ake zargin yana kuma da hannu wajen safarar kayan abinci da miyagun ƙwayoyi ga ƴan bindigan a maɓoyarsu daban-daban da ke a cijin dajin ta hanyar amfani da babur, rahoton The Cable ya tabbatar.

A cewar kakakin rundunar ƴan sandan kayayyakin da aka ƙwace a hannunsa sun haɗa da, bindiga ƙirar AK47 guɗa ɗaya, harsasan AK47, wayar salula guda ɗaya, kayan abinci da wani babur guda ɗaya wanda baya da rajista.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojin Sama Sun Yi Luguden Kan Maboyar 'Yan Boko Haram a Borno, Sun Sheke Manyan Kwamandoji Da Yawa

Ta yi bayanin cewa ana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin ba tare da ɓata lokaci ba, domin a gano tare da daƙile sauran hanyoyin da ƴan bindigan su ke samun kayayyaki, da cafke su domin gurfana gaban hukuma.

'Yan Binɗiga Sun Nemi Fansar N9m

A wani labarin na daban kuma, ƴan bindigan da suka sace wani babban basarake a birnin tarayya Abuja, sun bayyana kuɗin da suke so a mtsayin kuɗin fansa.

Ƴan bindigan dai sun sace dagacin na ƙauƴen Ketti tare da wani hadiminsa da kuma wani mutum ɗaya wanda tsautsayi ys ritsa da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng