Hukuma Sai Lallashi: Gwamna Ya Karbe Filin da Aka Ba Jami’ar Janar Ibrahim Babangida

Hukuma Sai Lallashi: Gwamna Ya Karbe Filin da Aka Ba Jami’ar Janar Ibrahim Babangida

  • Gwamnatin jihar Neja ta bada sanarwar karbe takardun mallakar filaye da aka ba wasu a baya
  • Wannan mataki da aka dauka ya shafi jami’ar IBB da ke Suleja da 3 Arms Zone a birnin Minna
  • Sabon Gwamna, Mai girma Umar Bago ya sa hannu ya karbe filayen kamfanoni da gidajen mai

Niger - Gwamnatin jihar Neja ta karbe takardun mallaka na CofO da aka ba jami’ar nan ta Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) a garin Suleja.

The Cable ta ce baya ga jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida, gwamnatin Umar Bago ta kuma karbe takardun filin da aka ba wasu kamfanoni.

An kafa asalin jami’ar IBB ne a garin Lapai a shekarar 2005. Janar Ibrahim Babangida mai ritaya wanda ta ci sunansa ya yi mulkin soja a Najeriya.

Gwamnan Neja
Gwamna Umar Bago ya rantsar da mukarrabai Hoto: @HonBago
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

CBN ta zama ATM din munafukan gwamnati: Shehu Sani ya bi ta kan korarren gwamna Emefiele

Sanarwa daga gwamnati

Sakataren din-din-din na ma’aikatar filaye da gidaje a Neja, Abdul Hussaini ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yammacin Asabar.

Abdul Hussaini ya ce an cin ma wannan mataki a sakamakon dokar da Mai girma Gwamna Umar Bago ya rattabawa hannu bayan ya shiga ofis.

Babban jami’in gwamnati yake cewa wadannan filaye da aka bada sun dawo hannun gwamnati.

Sauraren filayen da aka karbe

Kamar yadda rahoton ya bayyana, sauran filayen da abin ya shafa sun hada da na hukumar datsen ruwa da Sabon Wuse da 3 Arms Zone a Minna.

Haka zalika filayen aikin sabuwar hanyar bayan gari da kuma ma’aikatar kula da gandun jeji a garin Kontagora kamar yadda doka ta bada dama.

A jawabin da ya fitar, Daily Trust ta rahoto jami’in ya ce karbe filayen ya shafi Maximum Shelter a Suleja da filin kamfanin Cityscape a Dikko.

Kara karanta wannan

Da Dumi Dumi: Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Gwamnan CBN, Emefiele

Gwamnati ta kuma karbe filin wani gidan mai da yake kan titin Keteren Gwari a birnin Minna.

Har ila yau sabon gwamna ya bukaci jama’a su tuntubi ma’aikatar filaye da gidaje domin samun duk wani karin bayani da ya shafi wannan mataki.

Binciken Gwamnan CBN

An samu labari cewa ba abin mamaki ba ne dakataccen Gwamnan bankin CBN zai kara kwanaki a hannun DSS bayan cafke shi da aka yi a jiyan nan.

Za a nemi Alkali ya amince a cigaba da tsare Mista Godwin Emefiele har sai illa Masha Allahu. Babu aiki a Najeriya gobe, watakila Talata za a je kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng