Ka Kawo Hujja: ’Yan Sanda Sun Kalubalanci Tsohon Gwamna Matawalle Kan Ya Kawo Hujjar an Masa Satar Motoci
- Tsohon gwamnan jihar Zamfara ya bayyana halin da aka jefa ahalinsa bayan da ‘yan sanda suka farmaki gidansa don duba wasu abubuwa
- Ya ce an sace masa motoci da sauran kayayyakin amfani, wanda hukumar ‘yan sanda ta ce sam ba haka bane, basu dauki komai ba
- A wani sabon batu, rundunar ‘yan sandan ta ce Matawalle ya kawo hujja idan har yana da yakinin an shiga gidansa an sace masa kayayyaki
Rundunar ‘yan sanda ta kalubalanci tsohon gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara da bayyana hujjar an sace masa motoci, Daily Trust ta ruwaito.
Bayan samamen da aka kai masa a gidajensa da ke Gusau da Maradun, Matawalle ya yi ikirarin cewa an yi masa mummunar sata na kadarorinsa.
Batun da Matawalle ya yiwa ‘yan jarida
A wata hira da ya yi da BBC Hausa, tsohon gwamnan ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Ban taba ganin irin wannan wauta ba inda za a shiga gidan wani haka siddan ba tare da izini ba kamar muna rayuwa a cikin kasar da ba ta da doka.
“Ina Abuja babu wanda ya gaya mani cewa wata kotu ta ba da wannan umarni ko ta gayyace ni kuma na ki amsa.
“Babban abin bakin ciki shi ne, a gidana na Gusau, an karya duk dakunan matana, hatta hijabi sai da suka kwashe. An dauki har da tukunya duk an saka a mota an tafi da su.”
Babu jituwa tsakanin gwamna mai ci da tsohon gwamna Matawalle
A tun farko, gwamnan jihar Zamfara na yanzu ya zargi Matawalle da sace kadarori da kudaden gwamnati ba gaira babu dalili.
Wannan ya kai ga aka samu rashin jituwa a tsakaninsu, har ta kai ga batun ya je gaban hukumomin da ke bincike a yanzu.
Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamnan da kuma jami’an tsaron da ake kyautata zaton sun shiga gidajensa.
Mun kwato motoci masu tsada 40 a gidan Matawalle, gwamnatin Zamfara
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da kwato tsadaddun motoci har guda 40 daga gidan tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle.
Gwamnatin ta kwato motocin ne bayan ta tura jami'an tsaro zuwa gidajensa da ke a birnin Gusau da Maradum a jihar.
Gwamna Matawalle dai ya sauka a mulki ne bayan kammala wa’adi daya, inda ya sha kaye a zaben 18 ga watan Mayun bana.
Asali: Legit.ng