Yadda Naira Ta Sha Wala-Gigi a Hannun Godwin Emefiele da Sauran Gwamnonin CBN a Najeriya

Yadda Naira Ta Sha Wala-Gigi a Hannun Godwin Emefiele da Sauran Gwamnonin CBN a Najeriya

  • Naira ta yi raunin da bata taba yi ba tun bayan da Najeriya ta koma kan mulkin dimokradiyya kamar yadda ta lalace a karkashin korarren gwamnan CBN, Godwin Emefiele
  • Bincike ya nuna cewa darajar Naira ta ta taka mafi karancin daraja idan aka kwatanta da dala a kasuwar canji a hukumance
  • Shugaban kasa Bola Tinubu na Najeriya na fatan cewa, sabbin shugabannin da ya nada a CBN za su kawo mafita ga matsalar

Tabarbarewar darajar kudin Najeriya, Naira, a tsawon shekaru tara na zamanin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya kasance mafi muni a tarihin kasar.

Idan za a iya fayyace komai, zamaninsa ne mafi muni duba da zamanin gwamnonin CBN hudu da suka shude tun bayan da Najeriya ta koma kan turbar dimokradiyya.

Lokacin da Emefiele ya hau kan kujerar gwamnan a watan Maris na 2014, farashin canjin Naira zuwa dala a hukumance ya kasance N155, a cewar StatiSense.

Kara karanta wannan

Ni ba barawo bane: Sanatan APC ya sharbi kuka a majalisa, ya fadi sharrin da aka masa

Yadda Naira ta kasance a hannun gwamnonin CBN
Emefiele, Sanusi, Jpseph | Hoto: Bloomberg
Asali: Facebook

Sai dai kuma ya zuwa ranar Juma’a 9 ga watan Yunin 2023, daidai da ranar da Emefiele ya yi salla da kujerarsa, bayanai daga asusun FMDQ sun nuna cewa an rufe kasuwar Naira da dala Amurka akan farashin N472.50 kan kowacce dala 1.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na nuni da faduwar darajar Naira a hukumance da N317.5 ko kuma 204.83% idan aka kwatanta da dala a zamanin Emefiele na shekaru tara.

Naira a kasuwar bayan fage

Lamarin dai ya fi muni a kasuwar bayan fage fiye da darajar a hukumance ba, inda Naira ta fuskanci faduwar da bata taba yi ba a tarihi.

A lokacin da Emefiele ya zama gwamna, musayar Naira da dala ana yinsa ne a kan N167a kasuwar bayan fage, bayan shekaru tara, ta fadi 357.4%, inda ya zuwa ranar Juma’a ake siyar da dala 1 kan Naira N765

Kara karanta wannan

Abubuwa 4 Da Emefiele Ya Yi Da Suka Bata Wa Tinubu, Gwamnoni, Da Sauran 'Yan Najeriya Rai

Yadda Naira ta kasance a karkashin gwamnonin CBN tun 1999

Idan aka yi la’akari da yadda farashin Naira yake a karkashin shugabancin gwamnonin CBN daban-daban tun daga 1999, ya nuna cewa kowane gwamna ya fuskanci kalubale na musamman.

Duk da haka, matsalolinsu basu taba kasancewa masu sarkakiyar da suka kai tsakanin 2014 da 2023 ba.

  • Joseph Sanusi (1999 zuwa 2004): Farashin Naira da Dala a Najeriya ya karu daga N99 zuwa N132.
  • Chukwuma Soludo (2004 zuwa 2009): Farashin CBN na dala ya karu zuwa N146, yayin da ya kai N181 a kasuwar bayan fage tare da haifar da banbancin N35.
  • Sanusi Lamido Sanusi (2009 zuwa 2014): Farashin CBN na dala ya kai N155, inda a kasuwar bayan fage ya kai N167, wanda ya nuna bambancin N12.
  • Godwin Emefiele (2014 zuwa 2023): A lokacin Emefiele, dala sai da ta kai N463, yayin da a kasuwar bayan fage ta kai N765 tare da banbancin N301.

Kara karanta wannan

CBN ta zama ATM din munafukan gwamnati: Shehu Sani ya bi ta kan korarren gwamna Emefiele

Yau dai ta Emefiele ta kare a CBN, duk wani batu da zai iya biyo baya sai dai sharhi da kuma matakin da gwamnati mai ci za ta iya dauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.