ATM Din Munafukan Gwamnati: Shehu Sani Ya Ce Akwai Bukatar Yiwa CBN Wankin Soso da Sabulu
- An bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya fara aikin yiwa babban bankin Najeriya gaba dayansa wankin babban bargo
- Tsohon dan majalisar dattawa Sanata Shehu Sani ne ya yi wannan kiran ta shafinsa na Twitter a ranar Asabar, 10 ga watan Yuni
- Sani ya kuma zargi Emefiele da mayar da CBN zuwa na’urar cire kudi ta ATM ga masu kitse-kitse a gwamnatin da ta shude
Tsohon Sanatan Kaduna, Shehu Sani ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele.
Ku tuna cewa a baya Legit.ng ta rahoto muku cewa, an dakatar da Emefiele da daren ranar Juma’a, 9 ga watan Yuni, biyo bayan sanarwar da sakataren gwamnatin tarayya (SGF) ya fitar.
Dalilin da yasa aka dakatar da Emefiele
Wani yankin sanarwar gwamnatin tarayya ta dakatar da Emefiele ta ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin kasa, Mista Godwin Emefiele, CFR daga aiki ba tare da bata lokaci ba.
"Wannan ya biyo bayan binciken da ake yi a ofishinsa da kuma sauye-sauyen da aka tsara a fannin hada-hadar kudi na tattalin arzikin kasa."
Martanin Shehu Sani game da dakatar da Emefiele
Dangane da wannan lamarin, Sanata Sani ya bukaci shugaba Tinubu da ya tsaftace babban bankin yadda ya kamata ba wai kawai korar Emefiele ba.
Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:
“Dakatar da Emefiele abin a yaba ne, nada Shonubi a matsayin mukaddashin Gwamna ma abin yabawa ne.
"Amma aikin tsaftace gida kamar CBN zai yiwu ne ta hanyar shigar da tawagar masu binciken kudi daga WAJEN CBN.
“Su kadai ne za su iya yin bincike cikin kwarewa sosai a babban bankin su kuma fada wa kasar yadda aka tafiyar da bankin a karkashin kulawar Emefielen Buhari.”
Yadda Emefiele ya mai da CBN ya zama ATM din ‘yan kitse-kitse a gwamnatin Buhari
Shehu Sani ya kuma zargi tsohuwar gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da mayar da babban bankin ya zama ATM dinsu.
Sanata Sani ya ce:
"An yi amfani da CBN ne a matsayin ATM na munafukan gwamnati, kanti kuma saniyar tasan kwararrun ‘yan gaban goshi na gwamnatin da ta shude."
Ya kamata a kama Buhari da sauran wasu manyan kasa tare da Emefiele
A wani labarin, kunji yadda tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben bana ya bayyana bukatar a kama tsohon shugaban kasa Buhari.
Sowore ya ce, ba Emefiele ne kadai ke da laifi a jefa Najeriya bala’i ba, don haka ya kamata a kwamushe abokan cin mushensa.
Ya bayyana hakan ne jim kadan bayan da gwamnatin Tinubu ta bayyana dakatar da gwamnan na CBN ba tare da bata lokaci ba.
Asali: Legit.ng