Yanzu Yanzu: DSS Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta Ce Emefiele Na Tsare a Hannunta Don Bincike
- Hukumar DSS ta fitar da sabuwar sanarwa dangane da rade-radin da ake yi cewa dakataccen gwamnan CBN, Godwin Emefiele na tsare a hannunta
- Yan awanni bayan ta karyata batun, rundunar tsaron farin kayan ta ce yana hannunta tana bincike a kansa
- A daren ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni ne shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu ya sanar da dakatar da Emefiele
Dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, na tsare a hannun jami’an tsaro na farin kaya (DSS), jaridar The Cable ta rahoto.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar, Peter Afunanya ya fitar a ranar Asabar, 10 ga watan Yuni.
A yanzu Emefiele na tsare a hannunmu domin gudanar da bincike, DSS
Channels TV ta nakalto yana cewa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Hukumar tsaro na farin kaya (DSS) tana mai tabbatar da cewar Mista Godwin Emefiele, dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya yana nan tsare a hannunmu a yanzu saboda wasu dalilai na bincike.
"An umurtan jama'a, musamman kafafen yada labarai, da su yi taka-tsan-tsan wajen kawo rahoto da labarai game da wannan."
Hakan na zuwa ne yan awanni bayan DSS ta karyata rade-radin cewa Emefiele yana tsare a hannunta.
Da farko dai hukumar tsaron sirrin ta wallafa a shafinta na Twitter cewa: "Yanzu haka, Emefiele baya tare da DSS."
Legit.ng Hausa ta rahoto cewa Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele a ranar 9 ga watan Yuni, ya kuma bada umurnin a cigaba da bincike kan abubuwan da ya aikata lokacin yana gwamnan babban bankin na Najeriya.
Bai kamata Tinubu ya tsare Emefiele ba, Omokri
A wani labarin kuma, mun ji a baya cewa tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya ce bai kamata gwamnatin Bola Tinubu ta kulle dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Emefiele ba.
Omokri, a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, ya ba gwamnati mai ci shawarar cewa kada ta fara zargin Emefiele a bainar jama'a.
Har ila yau, Omokri ya gargadi shugaban kasa Bola Tinubu a kan tsare Emefiele ba tare da kariya ba.
Asali: Legit.ng