“Ina Godwin Emefiele Yake?” Omokri Ya Tsitsiye Gwamnatin Tinubu

“Ina Godwin Emefiele Yake?” Omokri Ya Tsitsiye Gwamnatin Tinubu

  • Reno Omokri, magoyin bayan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya shawarci shugaban kasa Bola Tinubu a kan lamarin Godwin Emefiele
  • Omokri ya ce bai kamata shugaban kasar ya hau ta kan Emefiele, dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ba
  • A cewarsa, kamata ya yi a ba Emefiele damar kare kansa idan har akwai wani zargi da ake yi masa

Abuja - Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya ce bai kamata gwamnatin Bola Tinubu ta kulle dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Emefiele ba.

Omokri, a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, ya ba gwamnati mai ci shawarar cewa kada ta fara zargin Emefiele a bainar jama'a.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Godwin Emefiele da Reno Omokri
“Ina Godwin Emefiele Yake?” Omokri Ya Tsitsiye Gwamnatin Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Central Bank of Nigeria, Reno Omokri
Asali: Facebook

CBN: Kada ka zama kamar Buhari, Omokri ga Tinubu

Har ila yau, Omokri ya gargadi shugaban kasa Bola Tinubu a kan tsare Emefiele ba tare da kariya ba.

Kara karanta wannan

"Bai Kamata Tinubu Ya Iya Dakatar Da Emefiele Ba": Fitaccen Lauya Ya Bayyana

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Omokri ya ce ya kamata Tinubu ya ba Emefiele damar kare kansa a kan duk wani zargi da za a yi masa.

Ya rubuta:

"Ina Godwin Emefiele? Kada gwamnatin Tinubu ta rufe yin zarge-zarge a kansa.

"Wannan shine abun da Buhari ya yi wa jami'an gwamnatin Jonathan jim kadan bayan ya karbi mulki a 2015. An rufe su, kuma yayin da suke tsare, sai aka yi ta zarge-zarge a kansu ba tare da an basu damar kare kansu ba."

Bugu da kari, Omokri ya bukaci shugaban kasa Tinubu da ya bari yan Najeriya su ji daga bakin Emefiele.

Omokri ya yaba ma shugaban kasa Tinubu

Ya yaba ma shugaban kasa Tinubu kan fara gwamnatinsa cike da nasara.

Har ila yau, Omori ya bayyana cewa bai kamata shugaban kasar ya ci gaba da gudanar da munanan ayyukan magabacinsa (Buhari) ba" domin wannan "yi daidai da abin da marigayi Sani Abacha ya yi, wanda ya sa har Tinubu ya yi gudun hijira a 1994."

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: DSS Ta Yi Martani Kan Zargin Kama Gwamnan CBN

Emefiele: Daga karshe DSS ta yi martani kan zargin kama gwamnan CBN

A wani labarin, mun ji cewa hukumar DSS ta ce dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, baya tsare a hannunsu.

Legit.ng Hausa ta rahoto cewa Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele a ranar 9 ga watan Yuni, ya kuma bada umurnin a cigaba da bincike kan abubuwan da ya aikata lokacin yana gwamnan babban bankin na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng